Cikin Sanyin Safiyar ranar asabar ne, 'yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky na Majalisin Jushi da ke cikin garin Zariya, suka yi aikin shara da tsaftace muhallin makwancin Mahaifiyar Jagoran Harka Islamiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).
Kabarin Mahaifiyar na Shaikh Zakzaky na cikin wani gida ne a unguwar na Jushi, a ranar 21/12/2015 Elrufa'i ya sa aka rushe gidan, bayan ta'addancin da sojoji suka yi a kan Jagoran, na kashe mutum fiye da 1000 daga almajirai, 'ya'ya da danginsa, da rusa gidansa da suka yi.
Nan wasu daga hotunan aikin gayyatar ne da ya gudana a safiyar Asabar
0 Comments