Dayammacin yau 6/1/2019 Alamajiran sayyid Ibrahim yaqub Al-zakzaky Academic forum na kaduna (Afmin kd chapter) suka shirya zikira hade da birthday na gawarazan shahidan academic forum na yankin kaduna.
Bayan bude taro da addu'a tareda karatun Qur'an anshiga bayani akan shahidin farko a jerin shahedan na academic forum Wanda kuma shine yake Jan ragwamar ita academic forum din a lokacinda yana raye (Shaheed rabi'u).
Shaheed rabi'u yakasance mutum mai yawan ibada da kokari akan duk wani abu da yashafi al'amarin jagora, kuma yakasance mutun mai Neman nakanshi da kokarin ganin yakarekanshi da chin haram, Bayan shahadar Shaheed rabi'u.
Shaheed Abdulmalik ne yamaye gurbin Shaheed Rabi'u wajan ganin yadabbaka abinda shahed rabi'u yatafi da burinsu.
Kamar yanda mahaifin Shaheed Abdulmalik yakefada wajan taron cewa: Abdulmalik yakasance mai matukar son shahada takai haryana fadawa mahaifiyarsa cewa yanzu gidannan ba shahidi ? Hmm to kubari kuga nine shahidi nafarko a gidanan.
Mutane dadama a wajan taron sunyi jawabai akan duka shahidan biyu *(shaheed rabi'u da shaheed Abdulmalik)* kama daga iyaye,abokani, yayyu, Abin burgewa kowa fada yake duk wadanan shahidan sun chanchanci shahada, yakamata suje suhuta.
Allah ta'ala yakarbi shahadarsu yakuma tabbatardamu tareda azurtamu da fitowar jagora sayyid zakzaky (h).
Free zakzaky
Free zakzaky
Allahprotectzakzaky.
0 Comments