Ad Code

Responsive Advertisement

Tashin Bom a birnin Basra ya shahadantarda mutane dayawa inda wasu da dama suka jikkata



_ Mutane da dama ne suka yi shahada yayin da wasu hudu suka jikkata sakamakon fashewar wani abu da ya afku a tsakiyar birnin Basra na kudancin kasar Iraki, in ji rundunar sojin kasar.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ayau Talata, ta ce wani babur da aka dankare da bama-bamai ne ya haddasa tashin bam, wanda ya haifar da wani bakin hayaki a sararin samaniya.

Wata kafar yada labarai ta tsaro ta Iraki, mai alaka da jami'an tsaron kasar, ta ce mutane hudun sun mutu sakamakon gobarar da ta tashi a wasu motoci biyu da ke kusa da babur din.

Saad Maan, shugaban Sashen Kafafen Yada Labarai na Tsaro, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce " Kwararru  na cigabada bincike har yanzu a wurin da abun yafaru domin sanin yanayinsa da kuma bayar da karin bayani game da yanayin hadarin."

A cikin wata sanarwa da wata majiya mai karfi ta jami'an tsaro ta shaidawa kafar yada labarai ta Rudaw ta ce fashewar ta faru ne daura da asibitin Al-Jumhouri da ke tsakiyar birnin kusa da mahadar Al-Samoud.

'Yan sanda da majiyoyin kiwon lafiya tun da farko sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa wasu mutane 20 sun samu raunuka a fashewar bom din.

_ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.

Post a Comment

0 Comments