Ad Code

Responsive Advertisement

Jirgin karkashin ruwa (Submarine) na sojan haramtacciyar kasar Isra'ila ya kama da wuta a tashar Haifa.


  – Wani jirgin ruwa na sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya kama da wuta tare da yin barna mai tsanani.

Jaridar Sahayoniyya a ranar Litinin ta bayar da rahoton cewa wani jirgin ruwa na sojan ruwan Isra'ila ya kama wuta a tashar ruwan Haifa.

A cewar rahoton, gobarar ta yi mummunar barna a cikin jirgin karkashin ruwa.

A cewar majiyoyin IZionist, hatsarin ya afku ne sakamakon kuskuren da daya daga cikin ma’aikatan jirgin da ke karkashin ruwa ya yi kuma ya yi mummunar illa ga ma’aunin wutar lantarki.

A wani lamari da ya faru watanni hudu da suka gabata, wani soja ya ji rauni a wata gobara da ta tashi kan wani jirgin ruwan yaki mallakar rundunar kwamandojin sojan ruwa ta Isra'ila.

_ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.

Post a Comment

0 Comments