KUN SAN NIMA ALMAJIRIN MALLAM ZAKZAKY NE, KUMA NA KOYI ABUBUWA DA DAMA DAGA RAYUWAR MALLAM ZAKZAKY.
---Inji Prince Deji Adeyanju
Daga Nasir Isa Ali
Yau ranar talata 25/12/2018 rana ce ta musamman ga duk wani kirista, kuma rana ce wacce kowanne kirista yake farin ciki da murnar haihuwar Yesu Almasihu.
Misalin karfe 11:30 na safiyar yau ne, 'yan'uwa musulmi almajiran Mallam Zakzaky suka kai wa d'an rajin kare hakkin d'an adam, Prince Deji Adeyanju ziyara a gidan kurkukun Kurmawa domin taya shi murnar bikin ranar kirsimati. Taron ziyarar wanda aka gudanar dashi a farfajiyar saman benen kurkukun dake bayan gidan sarkin Kano, ya samu halartar burazu da sistoci.
Bayan hawan da aka yi damu saman bene,sai muka d'an yi jira kimanin mintina 30, domin shi Deji din yana k'asa yana ganawa da wasu bak'in nasa. Da aka fad'a masa cewar ga almajiran Mallam Zakzaky can suna jiransa, sai ya katse wancan ganawar ya garzayo domin ganin mu.
Hawowarsa sama keda wuya, sai ya fara rungumar 'yan uwa maza yana gaisawa damu cikin tsananin kauna da soyayya.
Daga nan sai aka fara rera wak'en kirsimeti tare da shi Dejin ana shewa ana tafi, har su kansu masu gadin gidan yarin suka rika dariya da murna.
Bayan an gama gaisawa da shi da kuma wake-waken murnar taya shi farin ciki, sai Barrister Haruna Magashi ya gabatar masa da maqasudin ziyarar tamu da cewar "wannan ziyarar muna yinta ne a madadin Mallam Zakzaky (H) da kuma babban d'ansa Sayyid Muhammad Ibrahim Zakzaky. Haka zalika mun kawo maka wannan ziyarar ne a madadin duk wani d'an uwa da 'yar uwa almajiran Mallam. Barrister Magashi ya nuna masa alkakin (Cake) da alawa da ruwan Faro da aka kawo masa, sai ya sake yin tsalle ganin alkakin na dauke da rubutun 'Happy Christmas'.
JAWABIN DEJI ADEYANJU
Daga nan sai Deji ya fara jawabinsa.
Ya fara da cewar 'kun sanni sosai, kuma kun san cewar ni babban almajirin Mallam Zakzaky ne ko?
To Ku cigaba da duk abinda ake yi domin mu ne da nasara. Yace idan Buhari zai kwashe shekaru 15 yana mulki, to watarana dai zai sauka kuma tarihi ne zai rubuta ayyukansa.
Yace gashi nan duk muna rungumar juna cikin kauna da soyayya da girmama juna ba tare da yin la'akari da addini ko kabilarmu ba, to wannan shi ne d'aya daga cikin laifin Mallam. Idan kuka lura ai farkon duniyar nan duk mutane abu daya ne, amma da tafiya tayi tafiya sai shi mutum ya rik'a rarraba duniya zuwa bangare -bangare, sannan ya fara rarraba kan mutane da sauran duniya din, don haka mu mun san mu duka abu daya ne.
Deji ya k'ara da cewa wannan ziyarar da kuka kawo min ban san yadda zan nuna muku farin cikina ba, wallahi naji dadi sosai, kuna tsananin nuna min kauna.
Sakona zuwa ga 'yan uwa dake waje shine, ku fad'a musu cewa, ina nan cikin koshin lafiya da farin ciki, kai ku fada musu cewar ni nan na fisu jin dad'i, domin na san wata d'aukaka ce zata zo mana nan gaba don haka ne Allah yake yin amfani da makiyinmu wajen uzzura mana domin mu samu d'aukaka.
Mutane da dama sun same ni suna bani shawarar cewar, me yasa ba zan tafiyata Amurka ba? Saboda yanzu haka iyalina suna can kasar Amurka, don haka in tafi can in ji dadin rayuwata in huta mana? sai nace musu in nayi hakan Buhari zai daina zalincin da yake yi ne?
Don haka ba don kaina nake yin wannan fafutukar ba ina yi ne domin ku, domin al'ummar mu baki d'aya. Laifina kenan! Saboda muna fallasa irin zalincin da suke yiwa mutane.
Yaya za'ace gwamnatin k'asa bata da aiki sai kashe 'yan kasarta, kuma kowa yayi shiru, sannan a rik'a tunanin babu abin da zai faru?
Ina shaida muku cewar babu wani gyaran da Buhari zai kawowa 'yan Najeriya, domin yana mulki ne tare da haushin wasu a ransa, yana mulki k'ullace da wasu a ransa, kullum shi tunaninsa yaya za'ayi ya kama su, ko ya cutar dasu, to mai irin wannan tunanin ta yaya zai iya yiwa mutane wani aiki?
Ku kuma na saba baku shawara kuma zan cigaba da baku ita, ku tsaya kan abin da kuke yi na yin fafutuka cikin tsari da kiyaye doka, domin wannan ne ya hana su samun nasara a kanku, babu yadda basu yi ba domin su nuna wa duniya cewar baku bin doka, amma babu wanda ya yarda dasu.
Na sha fada cewa yau shekara uku da Buhari yayi muku wannan mummunan ta'addanci, amma an kasa nuna ko da sau d'aya inda kuka dauko wuk'a kuka cakawa koda d'an Sanda, tare da cewa kun san gidajensu da wuraren ayyukan su.
Don haka ku cigaba da wannan fafutukar, Insha Allahu mu ne zamu yi nasara.
Ba domin dokar gidan yari ta hana a dauki hoton wanda aka tsare ba, da yau mun cika duniyar Internet da hotunan wannan ziyara da bikin nan.
Amma don Allah ina rokon ku da ku yad'a wannan ziyarar sosai, ko tura ko ina ku nuna wa 'yan uwa cewar ina nan lafiya, cikin farin ciki da murna, kuma ina taya su murna baki daya.
Ku isar da gaisuwa ta zuwa ga Mallam Zakzaky, Sayyid Muhammad Zakzaky, Mallam Ibrahim Gamawa, Dr.Sunusi Koki da Abdullahi Musa na Abuja Struggle.
Bayan ya kammala jawabinsa ne, sai aka kawo masa abin yanka Alkali (Christmas Cake) ya yanka 'cake' din, sannan wurin ya sake barkewa da shewa da wakokin bikin kirsimati.
Daga cikin masu Ziyarar akwai Dk.Dauda Nalado, Kabiru Kabara, Alh.Saminu Yakasai, Alh.Kabiru K/Kwari da Barrister Haruna Magashi. Akwai kuma ni mai rahoton Nasir Isa Ali, da Abdullahi Madobi da sauran dimbin Yan'uwa.
Mun baro gidan kurkukun kimanin karfe 1:25
---
Nasir Isa Ali
-----------------
Media Forum Kano
25/12/2018
0 Comments