Ad Code

Responsive Advertisement

______SADAKA_____

________SADAKA_____


-Daga Manzon Allah(S) Yana cewa:- Yin Sadaka Yana Warware Shaidancin Shedanu Dari Bakwai(700).

-Haka nan Daga Manzon Allah(S) Yana cewa:- Sadakan Dare tana Kankare Zunubi Babba Kuma tana Saukaka Hisabi,Kuma tana Bishe Fushin Ubangiji.

__Menene Sadakar Dare? Sadakar dace Itace Sadakar da ake Bayarwa a Asirce.(Ba tare da An sani ba).

-Sadaka Tana kara Dukiya, kuma tana kara tsawon Rai.



*Yazo a Ruwaya Cewa:- Akwai wani Mutumin da kullum idan ya hau Bishiyar Gidansa Sai ya dauko Kwai na Tsuntsuwar da take Kwai a wannan Bishiyar.

Sai wannan Tsuntsuwar ta Kai kara wajen Allah kan Abinda wannan Mutumin keyi Mata.

Sai Allah yayi wahayi Ga wannan Tsuntsuwar da cewa, Idan Mutumin nan ya hau tsani Dan dauko wannan Kwai Daga Bishiyar to zai Fado ya mutu.

Washe Gari Sai ya Hau da Niyyar Daukar Kwai, sai yaji Anyi sallama, sai ya sauko ya sallami Wanda yazo, Bayan nan Sai ya hau Bishiyar nan ya cire Kwai din nan ya soya.

Sai Tsuntsuwar nan take Gayawa Ubangiji cewa, Ya Rabbi kace min Idan wannan Mutumin ya hau Dan Cire Kwai zai Fado ya Mutum Amma Kuma Hakan be faru dashi ba.

Sai Allah ya Bata Amsa da Cewa, Lokacin da Wannan Mutumin ya hau Dan Cire Kwai anyi sallama a kofar Gidansa, sai ya sakko, to wani ne ke Neman taimako shine ya taimaka masa Dan ni(Dan Allah), Ya Bashi Sadaka, shine ni Kuma na kara masa Tsawon Rai.

Dan haka karki damu zan kaiki inda Zaki samu Salama(Sai aka Kaita Saman Ka'aba.

Kamar yanda Yazo a Ruwaya cewa Tsuntsayen(Tattabara) Da suke a Makka(Ka'aba) to Jikokin wannan Tsuntsuwar ce.


-Cikin wani Bangaren Jawabin Allama Sayyid Zakzaky(H), kan Sadaka.

Post a Comment

0 Comments