Ad Code

Responsive Advertisement

Sojojin yahudawan sahyoniya sunkai wa Falasdinawa mummunan hari a yammacin gabar kogin Jordan.



Majiyoyin yada labarai sun sanar da cewa an gwabza tsakanin gwamnatin sahyoniyawan da Falasdinawa a birnin Nablus da ke cikin yankunan da aka mamaye, da sanyin safiyar yau Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarto cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Ahad cewa, sojojin gwamnatin sahyoniyawan sun kai farmaki kan birnin Nablus da ke yammacin gabar kogin Jordan da safiyar yau Lahadi.

Rahoton ya ce an gwabza kazamin fada tsakanin matasan Palasdinawa bayan harin da yahudawan sahyuniya suka kai Nablus. 

Sojojin yahudawan sahyoniya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da harsasai kan Falasdinawa.

A yayin da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Palasdinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa dangane da ci gaba da kai hare-haren wuce gona da irin na gwamnatin sahyoniyawan a yankin yammacin kogin Jordan.

A cikin wannan sanarwa, Hamas ta gargadi gwamnatin sahyoniyawan a kan mummunan sakamakon ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na yammacin kogin Jordan.

313 Resistance media.

Post a Comment

0 Comments