Ad Code

Responsive Advertisement

ZARIA STRUGGLE A RANA 17


.

.

A Daren Yau Laraba Zaratan Matasa Sun Sake Gudanar Da Muzaharar #freezakzaky A Garin Zaria.

.

Daga Ali Ibrahim Yareema

.

Kamar kullum yauma zaratan matasa sun gudanar da muzaharar #FreeZakzaky a cikin garin zaria , muzaharar ta yau an gudanar da ita ne a cikin daren yau laraba misalin karfe Takwas na dare Inda Aka Dauko ta tun daga kan randar tudun wada har zuwa kofar doka duk a cikin garin Zaria.

Muzaharar ta gudana cikin tsari da kuma nizami , kuma cikin izza babu razana ana tafiya cikin tsari an dauki lokaci ana dukan kwalta ana fadin free zakzaky Dole, koda aka kai kofar doka zaratan sunta zagaye shataletalen kofar dokar cikin izza tare da fadin #FreeZakzaky dole.

Bayan an kammala kowa ya watse saiga motar yan'sanda guda biyu sun iso kofan dokan hannayen su dauke da muggan makamai biddigogi da adduna da gorori,

.

An fara muzaharar lafiya an kuma tashi lafiya.

Post a Comment

0 Comments