Ad Code

Responsive Advertisement

MATASAN HARKAR MUSULUNCI NA SHIYAR ZARIA SUN KAI ZIYARAR TAYA MURNAN SHIGA SUBUWAR SHEKARA A COCIN BARIKIN YAN SANDA DAKE ZARIA .........



Daga  Ali Ibrahim Yareema


A safiyar yau lahadi 06/01/2019 ne Matasan Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) na shiyar Zaria suka kai ziyarar taya murnan shiga sabuwar shekarar miladiya a cocin barikin yan sanda dake Zaria, ziyarar ta samu halartan matasan harkar maza da mata. Yayin ziyar nasu kiristocin sun karbesu hannu bibbiyu tare da nuna farin cikin kawo musu ziyarar da sukayi, hakan ma yasa aka gudanar da addu'oi na musamman da nufin Allah ya zaunar damu da kuma kasar mu lafiya.

.

Jagorar tawagar yan Shi'an da suka halarci taron addu’ar, Ali Yarima ya bayyana manufar ziyarar da suka kai Cocin, inda yace hakan bai wuce don kara dankon zumunci tsakanin yan Shia da kiristoci.

.

A cewar Yariman dukkanin addinan biyu basu yarda da tayar rikici ko hankulan jama’a ba, inda yace addinan biyu suna koyar da soyayya da kaunar juna a tsakanin jama’a, haka zalika suna koyar da hadin kai da farin ciki, daga karshe yace Kiristoci ne mafi kusanci ga Musulmai.

.

“Bai kamata mu dinga kashe kawunanmu da sunan addini ba, Allah daya ne ya haliccemu, don haka ya zama wajibi mu zauna da juna cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, mu jajirce wajen tabbatar da wanzuwar farin ciki, tare da taya juna jimami, shugabanmu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya umarcemu damu zauna lafiya da kowa.” Inji Yariman.

.

Da yake nasa jawabin, shugaban cocin kuma babban faston cocin ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara, inda yace wannan ne karo na farko da yan Shi'an suka taba kai musu ziyara a cocinsu.

.

Daga karshe kuma yayi kira ga duk mabiya addinan biyu dasu gudanar da addinansu cikin bin dokokin addinan domin wanzar da zaman lafiya mai daurewa.

.

Bayan gudanar da addu’o’in ne suka yi sallama da kiristocin sannan suka koma gidajen su.

Post a Comment

0 Comments