Ad Code

Responsive Advertisement

KHATAMAR MAULUDIN MANZON ALLA (S) JIYA A POTISKUM


Angudanarda Khatamar Maulidin Manzon Allah (s)  gudana jiya a harabar Fudiyya Potiskum.

___ Farfesa Dahiru Yahaya daga Jami'ar Bayero Kano,
Ne babban bakon da ya gabatar da jawabi agurin,

__Bayan bude taro da addu'a da karatun Alqur'ani mai girma,  mawaqa ne sukaita kwararo baitukan yabon Annabi Muhammadu (s)

__Daga nan kuma an saurari jawabai daga bakin Malam Abubakar Muhammad Baba Gadar Talakawa da Shaikh Abdullahi Adamu (Chief Imam na Masallacin Jumu'ar Alhaji Umaru Kwalla).

__Sannan daliban Fudiyya Potiskum da 'yan caji-caji sun gudanar da Fareti da Kareti a wajen, wanda ya burge dukkan mahalarta.

___Bayan andawo daga Sallah,
Farfesa Dahiru Yahaya daga Jami'ar Bayero Kano shi ne ya kasance babban bako a wajen, ya kwarara jawabi mai ratsa jiki, mai dauke da dimbim darussa da tarin ilimummuka.
________________________
Daga____Jagoran gaskiya resistance media
Tare da Potiskum media watch ta hannun Ibraheem El'tafseer

Post a Comment

0 Comments