Ad Code

Responsive Advertisement

MAFITAR MUSULMI A NIGERIA AWANNAN HALINDA MUKE CIKI

MENE NE MAFITAR MUSULMIN NIGERIA A WANNAN HALIN DA MUKE CIKI? — Shaikh Ibraheem Zakzaky yace: "Bani bukatar na dauki lokaci ina mana bayanin yadda wannan kasa (Nijeriya) ta kasance. Kowa ya sani. Ko sai na ce muku ga halin da take ciki?
Sai na ce muku ba amana? Ba aminci a kan hanyoyi, bashi a gidaje bashi a sararin samaniya? Sai na fada muku cewa ba ruwan famfo, ba man fetur, ba wutar lantarki? Ko sai na fada muku akwai ramuka a kan hanya? Ko sai na ce muku ana fama da rashin aikin yi? Ko sai na ce muku dabi'u sun lalace? Duk kun san wannan. Kowa yana ji a jika! Ko sai na fada muku cewa makarantu ba komai, sun zama gidajen kadangaru? Ko sai na fada muku cewa asibitocin Kasar nan sun zama makasa, gidajen kisa, a kai ka a karisa ka!?... In ana maganan matsalolin kasar nan kowa ya sani, kuma kowa yana ji a jika. Amma yanzu mene ne mafita? Kwanan nan za a yi wani shiririta, wai zabe. Na san wadannan tsinannun, wadannan 'yan iska din! Ba wani zaben da za su yi. Wannan' ya'yan iskan, club din ya'yan banza, tsinannu, Allah Ya kara tsine musu. Mu kam wallahi bamu yafewa masu rike da al'amarin kasar nan ba! Bamu yafe musu ba. Allah (T) Ya sa su yi mummunan karshe a duniya. Allah Ya dauwamar da ya'yan banza a wuta. Hakkinmu kuma Allah Ya fitar mana. Bamu yafe ba Wallahi. Musibar da kuma muke zaune a ciki Allah Ya isa! Kuma muna rokon Allah (T) Ya gaggauta kawo mummunan karshen wadanda suke mulkin kasar nan. Nigeria ce kawai kasar da tsinannu suke mulki, sai fitaccen fasiki, dan iska ake ba mukami a kasar nan. Wanda basu san kowa da komai ba sai kawukansu kawai. Ba wanda za ka duba a cikinsu ka ga al'umma ta dame shi, su kansu kawai suka sani, yaci ya sha yai facaka, ya kwashe arziki ya kai kasar waje. Wai za su yi zabe. Yanzu abin takaici sai Kaga mutane ana kada su duuu" kamar shanu, wai za a yi zabe, ba wani zaben da za su yi. In ma zabe ne da wannan bakin da wancan bakin wane bakin kake so? Ka duba ka ga wannan baki ka kalli wancan ma baki. Ka dawo ka duba ko w

Post a Comment

0 Comments