_ Al’amura na ci gaba da tabarbarewa a jihar Nagaland da ke arewa maso gabashin Indiya bayan da jami’an tsaro suka yi kuskuren kashe fararen hula 14 a ranar Asabar, lamarin da ya haifar da mummunar zanga-zanga da kuma rufe makarantu.
Rahotanni sun ce, masu zanga-zangar da suka fusata sun yi jerin gwano zuwa sansanin sojojin Indiya da ke gundumar Mon a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi ta jifa da kuma kona yankunan da ke kusa da sansanin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani soja.
"Akwai gungun jama'a a waje suna ta jifa da duwatsu," a cewar wani jami'in tsaro daga sansanin, wanda ke kewaye da dimbin masu zanga-zangar.
Akalla mutane shida ne aka kashe a ranar Asabar bayan da jami’an tsaro suka harbe wata babbar motar da ke dauke da ma’aikatan hakar kwal (Coal), inda suka yi tunanin cewa ‘yan bindiga ne.
An kashe karin fararen hula bakwai a wani rikici da ya barke tsakanin mazauna yankin da jami’an tsaro a yammacin ranar Asabar.
Kisan wanda hukumomin yankin suka bayyana a matsayin wani shiri ne na jawo cece-ku-ce a Nagaland, yankin da ke fama da tashe-tashen hankula.
A cikin 'yan shekarun nan, kungiyoyin da ke dauke da makamai a jihar sun shiga tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin Indiya.
"Mutane sun fusata sosai," in ji Honang Konyak, mataimakin shugaban kungiyar Konyak, koli na kabilar Konyak da ke gundumar Mon da ke kan iyakar India da Myanmar.
"Jami'an tsaro, wadanda ya kamata su zama masu kare rayukan Al'umma, sun kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba," in ji shi.
Don shawo kan zanga-zangar, hukumomi sun dage dokar hana fita a garin Mon tare da hana intanet ta wayar hannu da sabis na SMS a daukacin gundumar saboda "damuwa da matsalar doka da oda".
Da yake halartar jana'izar mutanen da aka kashe, babban ministan Nagaland, Neiphiu Rio ya bukaci a cire Dokar Sojoji [Special Powers] ko AFSPA, dokar da ta ba sojoji ikon kamawa, 'yancin harbi ko kisa, da mamayewa ko lalata dukiya a cikin "guraren da tashin hankula ke faruwa.
A halin da ake ciki dai, kiran a soke dokar ta AFSPA na kara karfi, inda ‘yan siyasa da masu fafutuka da dama ke shiga cikin ayarin masu kiran asoke dokar.
_ Ibn Tukur Almizan.
313 Resistance media.
0 Comments