_ Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Sin na da niyyar gina sansanin sojojin ruwa na farko a tekun Atlantika, wanda zai ba ta damar ajiye jiragen yakinta daura da gabar tekun yammacin Amurka.

Jaridar Wall Street Journal [WSJ] ta ce Beijing na son kafa sansanin soji a Equatorial Guinea, wata kasa ta yammacin Afirka mai fadin murabba'in kilomita 28,000, kuma tana da yawan jama'a miliyan 1.4.  

Rahoton ya ce, mai yiwuwa kasar Sin na tunanin gina wani sansani a birnin Bata, birnin da tuni kasar Sin ta gina tashar kasuwanci mai zurfin ruwa. Hukumar ta WSJ ta kara da cewa, za a iya amfani da tashar jiragen ruwa da ke Tekun Atlantika don sake gyarawa da kuma gyara jiragen yakin kasar Sin, ba tare da wata shakka ba domin ta yi kaca-kaca da Washington.

Jaridar ta ruwaito wani babban jami'in fadar White House yana cewa Amurka ta gargadi Equatorial Guinea a bara cewa "wasu shiga cikin al'amuranda suka shafi ayyukan kasar China [Sin] za su haifar da matsalolin tsaro a kasar."

Kasashen Sin da Equatorial Guinea ba su ce komai ba game da wannan batu, amma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya tattauna da takwaransa na Equatorial Guinea Simeon Oyono Esono Angue a birnin Dakar na kasar Senegal a karshen watan jiya.

"Idan da kasar Sin za ta kafa tashar samar da jiragen ruwa, wannan , zai bambanta da yadda Amurka take zato. Zai amfani yankin ba tare da wata illa ba, "in ji jaridar  Global Times.

_ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.