__ Shugaban Majalisar Zartarwar Hizbullah Sayyid Hashem Saffiedine ya ce wasu jam'iyyun da suka yi imanin cewa zasu iya gurgunta 'yan Gwagwarmayata hanyar takunkumi " wannan wauta ne."

"Idan wasu mutane suna tunanin hakan zai iya raunana wannan gwagwarmaya ta hanyar kewaye, zabe ko takunkumi, to ina gaya musu: Ku wawaye ne, kuma wawaye," in ji Sayyed Saffiedine, yayin wani taro a ranar Lahadi a kauyen Babliyeh na Lebanon.

Ya kara da cewa irin wadannan mutane ba sa karanta tarihi kuma ba su san cewa Sirrinkarfinmu shi ne imani da kuma dogara ga Allah Madaukakin Sarki.”

A wani bangare na jawabin nasa, Sayyed Saffiedine ya jaddada cewa wadanda ke kulla makarkashiyar adawa da suna neman daidaita alaka tsakanin Beirut da Tel Aviv, yana mai jaddada cewa "Wannan aikin ba zai wuce ba kuma ba za mu amince da shi ba."

Idan muka koma watan Satumban 2020, Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain sun sanya hannu kan yarjejeniyar daidaitawa da "Isra'ila". Daga baya Morocco da Sudan sun sanya hannu kan irin wannan yarjejeniyoyin tare da gwamnatin “Isra’ila”. 

Falasdinawa sun yi tir da yarjejeniyar daidaita su, suna mai bayyana su a matsayin  "cin amana" ga manufarsu.

Wadanda suke kulla makirci a kan 'yan gwagwarmaya suna "mafarkin daidaitawa, kuma wannan shine ainihin [fuskarsu].

Jami'in ya kuma jaddada cewa kungiyar Hizbullah ta kuduri aniyar ci gaba da tinkarar makiya.

Jagoran ya kara da cewa "a yau muna rayuwa cikin ni'ima da nasara kuma ba za mu taba fuskantar wulakanci da rauni ba, don haka muna ci gaba da kan turbar gwagwarmaya da kuma tsayin daka don tunkarar makiya, kuma ba za mu ja da baya ba, sai dai kara karfi."

Sayyed Saffiedine ya kuma ce tawagar da ke adawa da kungiyar Hizbullah a kasar Labanon, wadda ke son "raba" al'ummar kasar ga kasashen ketare, "ba za a iya ba ta wani abu ba" kuma ba za ta iya magance matsalolin tattalin arzikin kasar ba.

Kasar Lebanon ta fada cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki da na kudi tun daga karshen shekarar 2019. Rikicin shi ne babban barazana ga zaman lafiyar kasar tun bayan yakin basasar da aka kwashe shekaru 15 ana yi a shekarar 1990.

Matsalar tattalin arziki da ta kudi galibi tana da nasaba ne da takunkumin da Amurka da kawayenta suka kakaba wa kasar Labanon da kuma tsoma bakin kasashen waje a cikin harkokin cikin gidan kasar Larabawa.

__ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.