__ Hukumomin "Isra'ila" sun saki wani fitaccen fursuna dan Falasdinu, makonni biyu bayan cimma yarjejeniyar sakin, wanda ya kawo karshen yajin cin abinci  na kwanaki 131, in ji wata kungiyar kare hakkin fursunoni.

Kayed Fasfous, mai shekaru 32, ya kasance a wani asibitin “Isra’ila” tun bayan kawo karshen yajin cin abinci da ya yi a ranar 23 ga Nuwamba.

Falasdinawa da kungiyoyin kare hakkin bil adama sun ce wannan al'adar ta musanta 'yancin bin tsarin da ya dace, wanda ke bai wa hukumar damar tsare fursunoni na tsawon watanni ko ma shekaru ba tare da ankaisu kotu ba. 

Kungiyar fursunoni ta Falasdinu, wata kungiya da ke wakiltar fursunoni na da da na yanzu, sun tabbatar da cewa Fasfous ya koma gida ne a yammacin gabar kogin Jordan ta hanyar wani shingen binciken sojoji da ke kusa da birnin al-Khalil da ke kudancin kasar a ranar Lahadi da yamma.

Daga baya, shafukan intanet sun nuna hotunan tsohon fursunan a keken guragu yana murnar dawowar sa garin Dura na kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Wafa na Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, Fasfous ya shafe shekaru biyar a gidan yari na Isra'ila ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba, kuma ya rasa kimanin kilogiram 45 na nayinsa a lokacin yajin cin abinci.

Halin da masu yajin cin abinci guda shida ke ciki ya haifar da zanga-zangar nuna goyon baya a duk fadin "Isra'ila" da suka mamaye Yammacin Kogin Jordan da Gaza a watan Nuwamba suna kara matsin lamba kan gwamnatin "Isra'ila" ta saki fursunonin.

Yajin cin abinci ya kasance ruwan dare a tsakanin fursunonin Falasdinawa kuma ya taimaka wajen samun sassauci da yawa daga hukumomin "Isra'ila".

Yanayin wadannan yajin cin abinci ya banbanta daga daidaikun mutane da ke nuna rashin amincewa da tsare mutane ba tare da tuhumar ba su daga kungiyoyin da ke kira da a inganta yanayin cell. Kusan 500 daga cikin Falasdinawa 4,600 da kungiyar "Isra'ila" ke tsare da su ana tsare da su a "tsarin siyasa" a cewar Addameer, wata kungiyar kare hakkin fursunonin Falasdinu.

_ Ibn Tukur Almizan.
313 Resistance media.