- Gwamnatin Shugaban kasar Amurka Joe Biden ta bayyana samuwar wasu sabbin jiragen sama marasa matuka, wadanda ake sa ran za a aikasu kasar China, in ji sakataren rundunar sojin sama Frank Kendall.

Cikakkun bayanai na sabbin jiragen na sirri ne, amma za a shigar da bukatar a ba su kudade domin cigabada aikin samarda wadannan jirage a cikin kasafin kudin shekarar 2022 da gwamnatin Biden za ta mika wa Majalisa a farkon shekarar 2022, in ji Kendall ga Politico.

Kendall ya yi wata hira a ranar Asabar yayin da ya halarci taron tsaron kasa a jihar California.

Politico ya ce shirin bayar da tallafin ya bayyana kudurin gwamnatin Biden na saka hannun jari a cikin irin wadannan tsare-tsare don ci gaba da yaki da kasar Sin, wanda manyan jami'ai suka yi ta kira a bainar jama'a a matsayin "barazanar ci gaba" da Amurka ke fuskanta.

Kendall ya bayyana cewa an kera sabbin jirage marasa matuka don yin aiki tare da jiragen sama kamar na Next Generation Air Dominance fighter da F-22 da F-35 da ake da su da kuma jiragen sama na B-21.

Kendall ya ce yana fatan kaddamar da Sabbin Jiragen guda biyu a cikin shekarar 2023.

Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.