Ad Code

Responsive Advertisement

Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa matashi a wani samame da suka kai a tsohon birnin Nablus.


 – Sojojin Isra’ila sun harbi wani matashin Bafalasdine a kai, a lokacin da ake gwabza fada a birnin Nablus da ke arewa maso yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye.

Kamfanin dillancin labaran Ma’an na Falasdinu ya bayar da rahoton wannan danyen aiki a ranar Litinin, inda ya bayyana wanda aka kashe a matsayin matashin saurayi, wanda ya rasa ransa a wani samame da sojojin suka kai a tsohon birnin Nablus.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya kira maharan na Isra'ila a matsayin "'yan sandan bakin iyaka na gwamnatin kasar. 

Hukumar ta yi ikirarin cewa an yi asarar rayuka ne, a lokacin da sojojin suka yi arangama da Falasdinawa, wadanda ke jefa bama-bamai a kan dakarun.

An kuma yi zargin cewa fadan ya barke ne bayan da sojojin suka kama wani Bafalasdine da ake nema ruwa a jallo.

Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta bayyana jimamin shahadar matasan a cikin wata sanarwa da ta fitar, amma ba ta bayyana shi a matsayin daya daga cikin mambobinta ba.

Har ila yau a ranar litinin sojojin Isra'ila sun kai farmaki kan sansanin 'yan gudun hijira na Al-Ain da ke Nablus da kuma birnin Bethlehem da ke yammacin tsakiyar gabar yammacin kogin Jordan.

Sojojin Isra'ila sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa Falasdinawa a yayin farmakin na karshe.

Lamarin dai na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da sojojin Isra'ila suka kashe wani matashin Bafalasdine tare da jikkata wasu da yawansu ya kai 68, inda suka kai hari a kudancin Nablus.

A shekara ta 1967 ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta mamaye yankin yammacin gabar kogin Jordan kafin ta fara sanyawa yankin Falasdinawa matsugunan da ba bisa ka'ida ba tare da tauye wa Falasdinawa yancin kai a can.

_ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.

Post a Comment

0 Comments