– Jiragen yakin kawancen da Saudiyya ke jagoranta sun kai farmaki kan wata unguwa a lardin Hajjah da ke arewa maso yammacin kasar Yamen, inda suka kashe akalla mutane uku ciki har da kananan yara biyu tare da jikkata wasu biyu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarto cewa, ya nakalto daga majiyar tsaron kasar Yemen cewa, harin da aka kai ta sama a ranar Lahadin da ta gabata ya kona wani gida a yankin Harad na Hajjah.

Wata majiya tace " wata mata mai shekaru 60 da ‘ya’yanta biyu,  sun mutu a harin, tare da raunata wasu mutum  biyu a cewar majiyar.

kawancen da Saudiyya ke jagoranta "suna kai wa fararen hula hari da kuma aikata laifukan yaki wadanda abin kunya ne ga bil'adama."

A ranar Asabar din da ta gabata ne jiragen yakin Saudiyya suka yi ruwan bama-bamai fiye da 50 a wasu lardunan kasar Yemen da suka hada da Ma'rib, Hudaydah da Sa’ada.

Kasar Saudiyya da ke samun goyon bayan Amurka da kawayenta a yankin, ta kaddamar da yakin kasar Yemen a watan Maris din shekarar 2015, da nufin mayar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Yemen Abd Rabbuh Mansour Hadi mai gudun hijira kan karagar mulki tare da murkushe kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah mai farin jini.

Yakin ya yi sanadin mutuwar dubban daruruwan 'yan kasar Yemen, tare da raba wasu miliyoyi da muhaansu, Haka kuma yakin ya lalata ababen more rayuwa na kasar Yemen tare da yada yunwa da cututtuka a can.

_ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.