Ad Code

Responsive Advertisement

CIKAKKEN RAHOTON TARON TUNAWA DA KISAN KIYASHIN ZARIA NA SHEKARAR 2015 DAYA GUDANA YAU A BABBAN BIRNIN TARAYYA ABUJA.


_ Banama kamar kowace Shekara 'yan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Zakzaky (h) sungudanar da taron tunawa da mummunan kisan kiyashin da Gwamnatin Najeriya ta aikata akan Almajiran Sayyid Zakzaky (h) a Husainiyya Baqiyyatullah da gidan Jagora Sayyid Zakzaky (h) dakuma Makabartar Shahidai ( Darurrahama ) dakuma Fudiyya Islamic Center, inda suka kashe 'ya'ya da 'yan uwa dakuma almajiran Sayyid Zakzaky (h) akalla Samada mutum 1000+ dakuma raunata wasu dadama inda har yanzu wasu kedauke da Raunukanda suka samu asakamakon wannan Ta'addanci na Gwamnatin Najeriya.

Taron Angudanardashi Yau Lahadi 12 gawatan December a babban birnin tarayya Abuja, taron yasamu halartar dimbin Almajiran Sayyid Zakzaky (h) daga sassan kasarnan.

Kadan daga cikin abubuwanda suka gudana awajen wannan taro sunhada da jawabai daga malamai da 'yan Gwagwarmaya daga sassan kasarnan dama kasar Ingila, dakuma mawaka dakuma Display, 
Mawakan Hiphop na Halal Boys sungudanara wakar juyayi, sannan sai Display daga 'yan Intizar dakuma 'yan Kasshafatu-Imamul Mahadi, sannan sai Alhaji Mustapha Umar baba gadon kaya yagabatarda waka, Sannan sai Lakca daga Farfesa Isah Hassan Mshalgaru daga jami'ar ABU, Sai Ruhi Rizvi daga kasar ingila, saikuma Dan rajin kare hakkin bil'adama Deji adyanju, saikuma Farfesa Abdullahi Danladi shima daga Jami'ar ABU, Saikuma Jawabin Maigayya mai aiki jagoran harkar Musulunci a Najeriya Sayyid Ibraheem Zakzaky (h) inda yagabatarda jawabi tahanyar kunna bidiyon jawabinshi.

Akarshe Dakta Sunusi Abdulkadeer Wakilin 'yan uwa na kano yarufe taron da addu'a.

Tarondai nayau yagudana ne a YESMIN EVENT CENTER kuma taron Zaicigaba a gobe Litinin a Fudiyya Maraba Abuja, inda za'aji jawabai daga wadanda suka tsira da rayukansu a wannan waki'a ta 2015.

__ Mahadi Tukur Almizan.

313 Resistance media.

Post a Comment

0 Comments