Ad Code

Responsive Advertisement

DARA TACI GIDA;Dakarun Saudiya sunyi luguden bama-bamai a sansaninsu a yankin Marib na kasar Yemen bisa kuskure.



_ Jiragen yakin kawancen Saudiyya sun yi luguden bama-bamai a wuraren da suka mamaye a lardin Marib na kasar Yaman, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuka da jikkata da dama daga cikin sojojin da Saudiyya ke marawa baya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarto cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Khabar Al-Yemeni cewa, jiragen yakin masarautar Saudiyya sun kai hari kan matsugunan su a lardin Marib bisa kuskure, inda suka kashe tare da raunata wasu da dama daga cikin mambobin rundunar hadin gwiwar.

Wannan dai ba shi ne karon farko da kawancen Saudiyya ke kai wa sansaninsu hari ba, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A baya-bayan nan ne mamba a majalisar siyasar kasar ta Ansarullah Muhammad Al-Bukhaiti a cikin wani jawabi da ya yi ya bayyana cewa, dakarun 'yan tawayen Yemen na dab da samun nasara ta karshe a birnin Marib.

Tun a ranar 26 ga watan Maris din shekarar 2015 ne Saudiyya tare da hadaddiyar daular Larabawa (UAE) tare da koren Amurka da kasashen yammacin duniya suka kai munanan hare-hare kan kasar Yaman tun daga ranar 26 ga watan Maris din 2015, da nufin maido da hambararriyar gwamnatin Hadi.

Jami'an gwamnatin ceton kasar Yemen sun sha nanata cewa sojojin kasar Yemen da kwamitocin jama'a za su ci gaba da mayar da martani kan hare-haren ta'addancin matukar dai kawancen Saudiyya ba zai dakatar da yakin da ake yi da kasar Yemen ba tare da kawo karshen wannan kawanya.

Dubun dubatar 'yan kasar Yemen ne suka jikkata tare da yin shahada a hare-haren da Saudiyyar ke jagoranta, inda akasarinsu fararen hula ne.

_ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.

Post a Comment

0 Comments