– Shugaban kasar Iran Ebrahim Raeisi ya yaba da rawar da shahidi Laftanar Janar Qasem Soleimani ya taka wajen kare yankin da duniya baki daya daga hadarin kungiyoyin takfiriyya.

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raeisi a jiya litinin ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da iyalan Laftanar Janar Qssem Soleimani domin tunawa da cika shekaru biyu da shahadarsa.

Shugaban ya ce Janar Soleimani ya taka muhimmiyar rawa wajen ceto kasashen Iraki da Siriya da ma sauran kasashen yankin daga hadarin ta'addancin takfiriyya.

Raeisi ya ce watakila har yanzu da yawa daga cikin musulmi ba su san irin kimar  wuraren ibada masu tsarki a Iraki da Siriya ba ga Iran, yana mai kira da tunawa ga masu kare Haramai masu tsarki wadanda suka samu horo daga shahidi Soleimani.

Shugaban ya yi nuni da cewa da ba don shahidi Soleimani ba, da yanzu yankin da ma duniya baki daya za su iya shiga cikin hadarin 'yan takfiriyya.

_ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.