Sojojin yahudawan sahyoniya na ci gaba da kai hare-hare a yammacin gabar kogin Jordan tare da shahadantarwa da jikkata fararen hula.

A harin da dakarun yahudawan sahyuniya suka kai yankin Ras al-Ayn da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan, wani Bafalasdine mai shekaru 31 ya yi shahada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarto cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-Youm cewa, dakarun yahudawan sahyuniya sun harbe shi a kirjinsa kai tsaye inda hakan yayi sanadin shahadarshi.

Yahudawan sahyuniya sun kama wani matashi Bafalasdine daga yankin kafin su yi arangama da mayakan Gwagwarmaya da dama dasuka jefa musu gurneti.

Majiyoyin yankin na Palasdinawa sun sanar da cewa, an kuma jikkata Falasdinawa biyar a harin, biyu daga cikinsu kuma an kama su tare da dauke su da wata motar sojan yahudawan sahyoniya.

Shugaban kungiyar Islamic Jihad Tariq Izzuddin ya ce a dangane da haka ne 'yan gwagwarmaya za su yi yaki da mamayar da yahudawan sahyuniya suka yi a garuruwan yammacin kogin Jordan da dukkan karfinsu.

__ Ibn Tukur Almizan.
313 Resistance media.