Ad Code

Responsive Advertisement

Gwamnatin Sahayoniyawan Isra'ila ta kama shugaban Hamas Sheikh Hassan Yousuf a yau Litinin

 – Sojojin yahudawan sahyuniya sun kama shugaban Hamas Sheikh Hassan Yousuf a gidansa da ke garin Beitunia kusa da birnin Ramallah da ke yammacin gabar kogin Jordan.

A safiyar yau litinin ne dakarun yahudawan sahyuniya suka kai farmaki gidan daya daga cikin shugabannin kungiyar Hamas dake yammacin gabar kogin Jordan.

Sun kama Sheikh Hassan Yousef, wanda shi ne wanda ya kafa kungiyar Hamas, inda suka tafi da shi wani wuri da ba a sani ba.

A halin yanzu yana aiki a matsayin daya daga cikin shugabannin Hamas a Yammacin Kogin Jordan. Youssef ya shafe fiye da shekaru 21 a gidan yarin Isra'ila.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Sahayoniya ta kame shugaban na Hamas makonni kadan bayan sakinsa daga gidan yari.

Kamen Youssef ya zo daidai da tsare 'yan kungiyar Hamas da ake yi a Yammacin Kogin Jordan a daidai lokacin da ake cika shekaru 34 da kafa kungiyar Hamas.

__ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.

Post a Comment

0 Comments