__ Wata kotu a Myanmar ta yanke wa hambararriyar shugabar kasar Aung San Suu Kyi hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.

Wani mai magana da yawun sojojin Myanmar ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an samu Suu Kyi da laifin tunzura jama'a da kuma keta dokokin COVID-19.

Zaw Min Tun ta ce ta samu zaman gidan yari na tsawon shekaru biyu a kan kowanne daga cikin laifuka biyun.

Hakazalika, an kuma daure tsohon shugaban kasar Win Myint na tsawon shekaru hudu a karkashin tuhume-tuhume iri daya, in ji shi, ya kara da cewa ba a kai su gidan yari ba tukuna.

"Za su fuskanci wasu tuhume-tuhume daga wuraren da suke tsare a yanzu" a babban birnin kasar Naypyidaw, in ji shi, ba tare da yin karin bayani ba.

Kamfanin dillancin labaran reuters da kamfanin dillacin labarai na Associated Press sun bayyana cewa, an yankewa Aung San Suu Kyi da Win Myint hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari ga kowannensu.

An rufe shari'ar a Naypyidaw ga manema labarai, yayin da sojoji suka hana lauyoyin Aung San Suu Kyi sadarwa da kafafen yada labarai da jama'a.

Hukuncin da aka yanke ranar Litinin shi ne na farko cikin kararraki goma sha biyu da sojoji suka shigar a kan Aung San Suu Kyi tun bayan da  suka hambarar da gwamnatin farar hula a wani juyin mulki a ranar 1 ga Fabrairu.

Sauran shari’o’in sun hada da tuhume-tuhume da yawa na almundahana, da keta dokar sirrin gwamnati.

Kasar Myanmar dai ta fada cikin rudani tun bayan juyin mulkin, inda zanga-zangar da rashin zaman lafiya ya barke bayan da sojoji suka yi wa ‘yan adawar kasar kisan gilla, wadanda ta kira ‘yan ta’adda. 

Jami’an tsaro sun kashe akalla mutane 1303, a cewar kungiyar agajin fursunonin siyasa.

Akalla masu adawa da juyin mulkin 354 kuma an yanke musu hukuncin dauri ko kisa, a cewar AAPP, ciki har da mai taimaka wa Aung San Suu Kyi, Win Htein, wanda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a watan Oktoba.

_ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.