Amurkawa sun fuskanci hare-hare kan sansanonin soji biyu da  Amurka ke amfani da su a Syria da ayarin motocin Amurka da ke Iraki, a daidai lokacin da ake kara nuna kyama ga Amurkawa a kasashen Larabawa biyu masu makwabtaka da juna.

A cewar SANA, an ji karar fashewar wasu bama-bamai a sansanin Al-Tanf, wanda ke kusa da kan iyakokin Syria da Iraki da Jordan, a yammacin Lahadi.

Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin da ya haddasa fashe-fashen ba. Babu wani sojan Amurka da ke sansanin da ya ji rauni ko kuma ya mutu.

A ranar 20 ga Oktoba, sansanonin Al-Tanf da Amurka ke jagoranta a kudancin Syria ya fuskanci hare-hare da jiragen sama marasa matuka da rokoki.

Ban da haka kuma, an kai wa sojojin mamaya na Amurka hari daban-daban a Syria da makwabciyarta Iraki, a daidai lokacin da jama'a ke ci gaba da nuna bacin ransu game da jibge sojojin mamaya na Amurka a kasashen na Larabawa biyu.

Tashar talabijin ta RT ta Larabci ta kasar Rasha ta nakalto majiyar kasar nacewa, wasu makamai masu linzami guda uku sun kai hari kan sansanin sojojin Amurka da ke lardin Deir Ez-Zor da ke gabashin kasar Siriya a ranar Asabar.

Majiyar ta kara da cewa, jiragen sama masu saukar ungulu na soji da dama sun yi shawagi a yankin bayan harin da aka kai a sansanin sojin Amurka da ke cikin tashar iskar gas ta Conoco.

Kawo yanzu dai ba a bayyana ko daga ina ce makamin ya fito ba. 

Da alamu dai ba a sami labarin asarar rai ba daga sojojin Amurkan da ke sansanin.

Sansanin na Conoco, inda mayakan Kurdawa tare da dakarun da ake kira Syrian Democratic Forces (SDF) ke zaune, an kai musu hari na karshe a watan Yuli da harsashi da rokoki.

Wannan dai shi ne jerin hare-hare na baya bayan nan kan sojojin mamaya na Amurka a yankin gabashin Siriya.

A ranar 1 ga watan Disamba, wani bam da aka dana a gefen hanya ya kai hari kan ayarin motocin da ke dauke da kayan aikin soji da kayan aikin sojan Amurka a lardin Hasakah da ke arewa maso gabashin Syria.

Sojojin Amurka sun jibge sojoji da kayan yaki a gabashi da arewa maso gabashin kasar Siriya, inda ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta bayyana cewa antura sojojin na da nufin hana rijiyoyin mai da ke yankin fadawa hannun 'yan ta'addan Daesh.

A wani wurin kuma a lardin Al-Qadisiyyah da ke kudancin kasar Iraki, an kai wani harin bam a gefen hanya a kan ayarin motocin da ke dauke da kayan aikin soja na sojojin Amurka a daidai lokacin da ake kara tada murya kan tsawaita zaman sojojin Amurka a kasar ta Iraki.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa kanfanin dillancin labaran Shafaq na kasar Iraki cewa fashewar ta afku a kusa da birnin al-Diwaniyah babban birnin lardin a ranar Lahadin da ta gabata, kuma ya yi sanadin asarar wata mota.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, wanda shi ne na baya bayan nan a jerin hare-haren da aka kai kan dakarun Amurka a Iraki a 'yan watannin nan.


_ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.