Daga Ibraheem El-Tafseer
Shaheed Shaikh Nimr Baqir Al-Nimr fitaccen Malamin addinin musulunci ne a kasar Saudi Arebiya, wanda yake bin Mazhabin Shi’a. An haife shi ranar 21 ga watan Juni na shekarar 1959, a garin Awamiyah dake gabashin kasar Saudi Arebiya. Shaheed Shaikh Nimr Malamin Shi’a ne mai zurfin ilimi, wanda baya goyon bayan zalunci da azzalumai. Gwamnatin kasar Saudi Arebiya ta matsa masa matuqa kan yadda yake fallasa irin baqin zaluncin da hukumomin Saudiya suke yi. Ya shahara sosai wajen fayyace gaskiya komai dacinta, ba shi da tsoro ko kadan. Gwarzo ne namijin gaske, don kuwa bakinsa baya shiru muddin ya ga ana zalunci.
Gwamnatin kasar Saudi Arebiya ta kama shi a shekarar 2006, wanda ya ce, ya sha duka sosai a hannun ‘yan Mabanith. Shaikh Nimr ya gayawa gwamnatin Saudiya cewa “idan har baza su dinga mutunta ‘yan Shi’ar da suke gabashin Saudiya Arebiya ba, to su kore su mana daga yankin” shi ne sai gwamnatin Saudiya ta kama shi tare da almajiransa guda 35 a shekarar 2009. A lokacin da aka yi zanga-zanaga a kasar Saudi Arebiya a shekarar 2011 zuwa 2012, Shaikh Nimr ya fadawa masu zanga-zangar cewa “ku jure dukkan harsashin da ‘yan Sanda za su harbe ku da shi, sannan kar ku yi shiru, ku ci gaba da bayyana irin zaluncin da gwamnatin Saudiya take yi, gwamnatin Saudiya tana daf da rugujewa, muddin wannan zaluncin ya ci gaba”
A watan Juli na shekarar 2012, ‘yan Sandan kasar Saudi Arebiya suka harbi Shaikh Nimr a qafa, sannan suka kama shi. Sai kuma ‘yan Sandan suka fitar da sanarwar qarya, cewa wai sun kama shi ne a wajen musayar wuta da suka yi, tsakaninsa da su ‘yan sandan. ‘yan Sanda sun bude wuta sosai akan dubbunnan mabiyansa, masu nuna Alla-wadai da kama shi da gwamantin Saudiya ta yi, inda suka kashe mutane dayawa. A wannan kamun da gwamnatin Saudiya ta masa, ta gana masa azaba sosai, har sun yi amfani da lantarki wajen cutar da shi. Shaikh Nimr sai ya fara yajin qin cin abinci, a ranar 21 ga watan Agusta, wanda hakan yasa ya fada rashin lafiya matsananciya.
Kungiyar kare hakkin dan’adam ta ‘Asharq Center for Human Rights’ ta nuna damuwa matuqa akan halin rashin lafiya da Shaikh Nimr ke ciki, inda ta nemi hadin kan kasashen duniya domin iyalansa, ‘yan’uwansa, Lauyoyinsa da ‘yan rajin kare hakkin dan’adam a barsu su gana da shi. A ranar 15 ga watan Oktoba na shekarar 2014, gwamnatin Saudiya ta yankewa Shaikh Nimr hukuncin kisa. Sannan gwamnatin Saudiyan ta kama yayan Shaikh Nimr din, mai suna Muhammad Al-Nimr, saboda ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, gwamnatin Saudiya ta yankewa Shaikh Nimr hukuncin kisa.
A ranar 2 ga watan Janairu na sabuwar shekarar 2016, gwamnatin Saudi Arebiya ta kashe Shaikh Nimr tare da almajiransa 46, ta hanyar rataya. Wannan kisan da gwamnatin Saudiya ta yi wa Shaikh Nimr, kasashe da dama sun yi Alla-wadai dashi, sannan sun sha suka daga ‘yan rajin kare hakkin dan’adam na duniya. An kashe shi ne saboda kawai shi dan shi’a ne. A watan March na shekarar 2017 jami’an tsaron Saudiya suka je garinsu Shaikh Nimr din, Awamiyah, suka kashe ‘yan’uwansa guda biyu a gona, Miqdad da Mohammed Nimr. Sheikh Nimr ya yi karatunsa na addini a kasashen Iran da Syria.
Allah ya karbi shahadarsa, ya gaggauta hukunta wadanda suka kasheshi.
#FreeZakzaky
👇👇👇👇👇👇
👇👇👇👇👇
0 Comments