A ranar Litinin 31/12/2018 ne wakilin 'yan uwa musulmi almajiran Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) na garin Gombe, Shaikh Muhammad Abbari ya ziyarci Da'irar Dukku.
Da yake ganawa da 'yan uwa a yayin ziyarar Shaikh Abbari yayi kira ga 'yan uwa da sanya tsoron Allah a cikin dukkan al'amuransu, domin samun kusanci da Allah (T). Daga nan sai Shaikh Abbari ya fara nasiharsa dangane da halin da muke ciki a Harka Islamiyya. Malamin ya bayyana wadan nan kwanaki na bayan waki'ar 12/12/2015 a matsayin ranakun jarrabawa mai tsanani, babu abinda zayyi saurin tsallakar da dan uwa ya cinye wannan jarrawa kamar ya waiwayi waki'o'in da suka gabata. Haka nan fitintinu da muke fama da su a cikin gida idan dan uwa ya nazarci fitintinun da suka gabata da kyau ba zai dimauce ba. Kuma bai kamata dan uwa ya zama mai tallan fitina ko yawo da jita-jita ba. Kai wanda aka kawo ma labarin wata fitina ko jita-jita to kayi ma wanda ya kawo maka nasiha, ko ka je ka gano abunda ya gaya maka domin ka tabbatar da gaskiya.
Shaikh Abbari ya bukaci 'yan uwa da kowa yasan irin baiwar da Allah (T) yayi masa domin yayi ampani da wannan baiwar wajen ci gabantar da wannan Harka gaba. Zakaga wani wa'azi ya iya, wani aiki ya iya, wani infaki ya iya to kowa ya tsayu da aikinsa kamar yanda yakata.
Da yake bayani dangane da gwagwarmayar Abuja, Shaikh Abbari ya bayyana wannan gwagwarmaya na Abuja amatsayin muhimmin aiki na 'yan sa kai, domin ba Shaikh Zakzaky (H) ne yayi umurnin aje a tare a Abuja ba, to amma a yayin da Shaikh Zakzaky ya samu labarin wassu 'yan uwa sun tare a Abuja yayi farin ciki sosai domin yin hakan fito na fito ne da zalunci, kuma ta irin wannan hanya ne ake kawar da zaluci. Yayin da Shaikh Zakzaky yaji 'yan uwa a Abuja suna fadin "we are never surrender har abada" sai yace "alhamdu lillah lallai idan har 'yan uwa sun dake basu gaji ba kuma basuyi surrender ba to zalunci zai kau cikin sauki"
To tunda munga jagoranmu yayi farin ciki da wannan aikin to ya kamata mu kara kaimi a kai. Kuma wannan ba shine farkon abunda 'yan uwa suka kirkira Malam (H) ya karba ya sanya masa albarka ba, misali kamar aikin harisanci. Asalin harisanci wassu 'yan uwa ne suka baiwa Malam kariya a wani taro, an tashi taro kowa ya taso dole sai ya gaisa da su Malam (H) hannu da hannu, sai wassu 'yan uwan suka tare. Da Malam yazo shiga mota sai yace musu "HURRAS KENAN" shike nan daga lokacin sai aka tsara aikin harisawa. To haka nan tattaki, asalinsa 'yan uwa na Samaru ne suka tattako daga Samaru zuwa Husainiyya a ranar 40, da aka gayawa Malam Zakzaky sai yayi farin ciki, kuma yace "abun yayi kyau domin zai isar da sako" to da shekara ta juyo sai Kaduna suka tattako, da shekara juyo sai Kano, to sai ko'ina akayi harama. To sai Malam (H) ya bada shawarin duk masu sha'awar yin tattakin to a sanyawa ko wace hanyar shiga Zariya mikati, kar yazama kowa daga garinsu zai taso.
To shima Abuja struggle ba Malam Zakzaky (H) bane yayi umurnin muyi ba, amma da muka fara shi ya ji dadi harma yace wannan shine fito na fito da zalunci.
Dangane da Abuja struggle kuma ina kiranmu da abubuwa guda uku (3)
1- mutsaya kem! Karmu gaji. Wannan abunda ya faru a tattakin 40 a Abuja ya tabbatar mana cewa idan har bamu gaji ba to zalunci zai kau a cikin sauki. A ranar farko sun kashe sama da 'yan uwa 40 sai washe gari muka kara fitowa suka kashe 5, washe gari muka sake fitowa. A ranar ta3 kawai sai dai muka ga sojoji da 'yan sanda a gefen hanya sun sunkui da kan Bindiga kas muna wucewa cikin izza sun koma gefe suna kallonmu.
Kuma irin haka shi yake basu tsoro kan abunda suke son aikatawa akan jagoranmu, ai kunji zantukan El-Rufa'i ko? Na2
2- muna isar da sako ga mutanen dake cikin garin Abuja, jakadun kasashen waje da sauran baki da manyan ma'aikata domin Abuja itace babbar matattarar manya a Najeriya.
A farkon fara wannan struggle din idan mun fito mutane gudu suke ana ta watsewa ana rurrufe shaguna da gidaje, don ba'a saba ganin muzahara a Abuja ba. To amma yanzu idan mun fito ta ko'ina jinjina ake mana ana karban hotunan Shaikh Zakzaky (H) har ya zama yanzu kullum sai mun gurza hotuna kafin mu fito, saboda idan mun fito bama komawa gida da hotunan.
3- muna bukatar 'yan uwa na wannan yanki su tsayu da kansu wajen gudanar da al'amuran harka a cikin garin Abuja.
Kamar wadan da suka kaura suka dawo Abuja da zama to muna kokarin samar musu sana'o'i, wanda kuma hakan zai tabbata ne ta hanyar gudummawar mu don ba wani ne zai zo yayi mana ba. Inji Shaikh Abbari
Da yake magana da 'yan uwa dake a gida basu samu damar zuwa Abuja ba. Shaikh Muhammad Abbari yayi kira da cewa duk dan uwan da bai samu kasancewa a Abuja ba to Abuja struggle tana bukatar taimakonsa na ya dauki nauyin zuwan wani a madadinsa, ko ya tura taimakonsa, ta yanda zai zama anyi musharaka da shi. Idan duka uku (3)
1- zuwa da kanka
2- tura wakilci
3- tura taimako
basu samu ba to don Allah kar a manta Abuja struggle a cikin addu'a, kamar yanda Shaikh Zakzaky (H) yace kullum yana yi mana addu'a har a cikin sujjadar salla. Kuma dai insha Allahu bazamu bar Abuja ba matukar Malam na tsare.
___-Shaikh Muhammad Abbari
®-Umar Babagoro Dukku
0 Comments