👇👇👇👇👇👇
1) Ka Kama Hanyar Allah Kyam ko
da za ka yi asarar duk Duniyar
nan ne.
2) Ka Sadaukar da Kanka da
Dukiyarka ga Wannan Harka ta
Tajdidin Musulunci.
3) Ka yi wa Kanka Tarbiyya ta
Yadda za ka Siffantu da Siffofin
Addinin a Zantukanka da
Ayyukanka.
4) Ka Himmatu Wajan Neman
Ilimin Addini da Aiki da Shi.
5) Ka Guji Zaman Jagwab, ka
Nemi Sana'ar da za ka yi.
6) Ka ji Tsoron Yawo da Tsegumi,
ka Kuma Kwabi mai yin Hakan.
7) Kar ka Sanya Kanka cikin
Rigingimun Mazhabobi, abin da
ya Hada mu yafi Karfin Mazhaba.
Rawani abin Girmamawa ne,
in ka sa ka Alamtu da Addini a
Zantukanka da Ayyukanka.
9) Kar mu Ba Da'awarmu Wata
Sura ta Cewa mu Siyasa ce ta
dame mu.
10) Lalle ne Da'awarmu ta zama
tana Dauki dai-dai ne, Ba ta jawo
Mutane duuuu ba.
11) Ya Kamata Da'irori su Rika
Tsirowa ne, Amma ba a Rika Kafa
su ba Kamar na "Yan Wa'azin
Kasa baki daya.
12) Ya Zama ka Shiga Wannan
Harkar ne Domin ka Tsamar da
Kanka Daga Fushin Allah Ranar
Gobe Kiyama.
-
-
Domin Samun Cikakkiyar
Fahimtar Wadannan Nasihohin
ka Nemi Jawaban Sayyeed [H] na
Ijtima'o'in Kano da Zariya.









0 Comments