-------Sheikh Ibrahim yaqub El-Zakzaky jagoran Harkar Musulumci a Nigeria(IMN) Mutum Ne daya shahara akan Fafutikarsa Wajen Rashin yarda da yaqar Zalumci ,Danniya,Tsaurarawa ,Rashin Adalci da duk Wani Nau'in Zalumci
Sheikh Zakzaky Yana Nuna tsantsar Goyon Bayansa Ga duk Wadanda aka Zalumta a duk Inda Suke a Fadin Duniya Batare da La'akari da Al'adarsu yarensu ,Addininsu ko Fahimtarsu Ba .

Sheikh Zakzaky Mutum Ne Mara tsoro Akan Fadin Gaskiya koda akan waye ,duk Mulkinka ko Talakancinka Sayyed Zakzaky Zai Fadi Gaskiya Akanka Matuqar Ka Saba Bakayi daidai ba ,Bazaiji tsoron Komaiba
Sheikh Zakzaky ya Sadaukar da Komai Nasa A Qoqarinsa Na Fafutikar Ganin Ya Yantar da Wanann Al'ummar Daga Kangin Bauta,Danniya Da Zalumcin Turawan Mulkin Mallaka da Sukema Wannan Al'umma,Tun Bayan Rushe Daular Daular Musulumci ta Mujaddadi Sheikh Usman Bn Fodiyo daya kafa a Nigeria da turawa sukayi tare da Rushe Dokokin Allah (AlQur'an) A Matsayin Wanda Za'ayi Hukumci Dashi Da Maye Gurbinsa da Littafin Tsarin Yahudawa(Constitution) amatsayin Abun yima Biyyaya,
Da Wadannan Dalilan ne Sayyed Zakzaky ya tashi domin Kawo gyara da Sauyi a Cikin Zukatan Al'umma Zuwa Ga Tsarin da Zaizama Mafita Garesu Daga Mulkin Kama karya Na Zalumci da Suke .Ciki ta Hanyar Kira(Da'awa)domin a Koma Ma Tsarin Addinin Allah A tabbatar da Dokokin Allah a doron Kasa da dayin Biyayya Garesa Kamar yanda Allah ya aiko Annabi Muhammad (S.a.w.w) zuwa ga Mutane Dayin tawaye gaduk Tsarin Daya sabawa Na Allah ,Lallai Tsarin Musulumci shi zai kawo Adalci da Gaskiya da Zaman Lafiya da bayar da Haqqi ga Kowa Batare da La'akari da Addini ko Kabilarsa ba.

Sheikh Zakzaky ya kwashe shekaru Sama da 40 yana Batare da An sameshi da Laifi tashin Hankali ,ko taaddanci Ba shida duk Mabiyansa
Wannan yunkuri na Ganin Addinin Allah ya kafua doron kasa da yaqar Zalumci da Goyon Bayan Raunana sune dalilin dayasa Gwamnatocin Nigeria Suke Burin kasheshi tun farkon Fara Wannan kira , Bisa wannan ne yasa Gwamnatin Nigeria take cigaba da kashe Mabiyansa a Fadin Nigeria
A shirin Gwamnatin Nigeria karkashin General Muhammad Buhari Na Kawar da sheikh Zakzaky da Da'awar Bisa Kwangilar America, Isra'il da Saudi arebia Suka Shirya Kai Farmaki,da kaddamar da Ta'addanci akan jagoran Harka Sayyed Zakzaky Ranar 12/12/2015 a Garin Zaria.Inda suka kashe Sama da Mutum 1000+ciki harda yayan Sheikh Zakzaky guda shida tare da rushe duk wani Gini Mallakin Sayyed Zakzaky da Harkar Musulumci Wadanda Suka hada da Makaranta Gida,Da Cibiyar Bayar da karatun Addini (Hussainiyya Baqiyyatullah)Zaria da rushe Kaburburan Almajiran Sayyed Zakzaky da aka bizne a Makabartar shahidai (Darur Rahma) ,tare dayin kabarin Bai daya Ga Sama da Mutum 347 a Mando Kaduna state Domin Rufe shaidar adadin Almajiran Sayyed Zakzaky da Gwamnatin Nigeria ta Buhari ta kashe a Yayin Wannan Harin Wanda General: Tukur Yusuf Burutai ya Jagoranta, Da kama Daruruwan Almajiran Sayyed Zakzaky yana tsare dasu agidajen Yari BisaZalunci .

Dayin ruwan wuta akan sheikh Zakzaky da Matarsa Malama zeenatu ,Bayan kashe Masu yaya Guda shida Aka kamasu Cikin Mawuyacin Hali Na Rashin Lafiya Sakamakon Harbin Bindiga da Sojojin Nigeria sukayi Masu a Kusan dukkan sassan jikinsu ba tare da ankaisu asibiti ba babu cikakkiyar kulawar kwararren likita dukda Mawuyacin Halin da suke ciki na rai kwakwai Mutu kwakwai ,ana tsare dasu Hannun Hukumar jami'an tsaron farin kaya ta DSS Karkashin yusuf Magaji Bichi Bisa Zalumci dukda Umarnin da Babbar kotun tarayya Abuja ta Bayar Ranar 2/12/2016 Na cewa a sakesu kuma a Biyasu diyyar Naira Million Hamsin(50Million) Sannan a Gina Masu gidansu a duk Inda suke so A dadi arewacin Nigeria ,Amma Beam Buhari tayiwa Hukumcin kotu Karen tsaye taqi.

bin umarnin kotu har yanxu Rana cigaba da tsare sheikh Zakzaky tare da Matarsa Bisa Zalumci fiye da shekara uku duk wanna ta'addanci sunyi shine da sunan wai tare Hanya. Wanda Daga Baya yarima Mai jiran Gado Na Saudi Arebia Muhammad Bn Salman ya fito ya bayyanawa Duniya cewa sune suka sanya akayiwa sheikh Zakzaky Wannan ta'addanci Domin daqile yunkurinsa Na Mayar da Nigeria jamhuriyar Musulumci kamar Iran.

Tare da tilastawa Almajiran Sayyed Zakzaky daukar Makami domin bada dama Ga yahudawan America da Israel domin Zuwa satar Dukiyar Nigeria da sunan kawo tsaro da kawo Zaman Lafiya, Wanda Hakan Bai samuba sakamakon Matakan da Almajiran Sayyed Zakzaky suka dauka na Hakuri da Bin hanyoyin da suka dace domin Neman Haqqinsu Wanda dokar kasar taba kowane Dan kasa ,na Muzaharorin Lumana da Bayyanawa Duniya tsantsar Zalumcin Gwamnatin Nigeria akan Harkar Musulumci ta hanyar Rubuce rubuce da Fira da yan jaridu da Zuwa kotu Ciki kuwa Harda kotun Duniya dake Hague (ICC)Domin Neman Haqqi da Adaci akan Wannan Zalumci da Gwamnatin Buhari yayi,
Babban Laifin Sheikh Zakzaky da Almajiran Sa Ga Gwamnatin Nigeria Shine Sunce Bazasubi Tsarin daba Na Allah ba Kuma sunyi Masa tawaye .
Muna kira Na Musamma Ga Hukomomi na kasa da kasa da Masana akan Haqqi. Dan'adam da Masu ruhin tausayi da Adalci da Masuyiwa Nigeria Fatan Alkhairi da su Fito su Yaqi Zalumcin Gwamnatin Buhari da takeyiwa Sheikh Zakzaky Da tilastawa gareshi akan Sakin jagoran Harkar Musulumci sheikh Zakzaky Daga tsarewar Zalumci dayake Masa ,Cigaba da Tsare Sheikh Zakzaky Bazai Haifarwa Nigeria da Da Mai ido ba.

Rayuwarmu Fansar ta Jagoranmu Ce ,

A saki sheikh Zakzaky kawai.