"Kun san a nan muna ta fama da mutane su gane ME? Su kuwa basu gane ME, sun fi gane WA? Kullum ai ta darga da su, ba WA za ka ce ba ME? ME ke mulki? Ba WA ke mulki ba. Domin idan ME bai canza ba, to WA ba a bakin komai yake ba.
"Idan me na nan, to da Buhari, da Shagari, da Olushegun, da Jonathan da Dan-Adua, duk daya ne, idan dai ME din daya ne. Amma kaga WA daban-daban ne, ko da wannan Buhari, Shagari, ko da kaji ri-ri amma daban-daban ne.
In dai ME bai canza ba, to WA bai ce komai ba.
"To, yanzu mutane kamar suna cikin wani hali na neman Waye zai yi Shugabanci kuma Meye zai yi Shugabanci, ko? To, Matsalar kasar nan ba WA ke mulki bane, ME ke mulki din ne matsalar."
— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).
0 Comments