Zanga-zangar adawa da Sabbin Takunkumi na COVID-19.

'Yan sandan Belgium sun harba hayaki mai sa hawaye da kuma ruwan zafi don tarwatsa masu zanga-zangar adawa da matakan tilastawa da gwamnati ta kakabawa mutane saboda annobar ta Corona.

Dubban masu zanga-zangar ne suka fito kan tituna a Brussels inda suka yi tattaki zuwa hedkwatar kungiyar Tarayyar Turai [EU], suna ta rera taken "yanci" da kuma yin wasa da wuta.

Rahotanni sun ce, abin da ya faro a matsayin zanga-zangar lumana ya koma tashin hankali lokacin da aka hana masu zanga-zangar zuwa zagayen da ke wajen ofishin kungiyar Tarayyar Turai ta hanyar shingen waya da kuma yawan jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma.

Yayin da jirage marasa matuka biyu da wani jirgi mai saukar ungulu suka zagaye sama da kasa, rahotanni sun ce wasu masu zanga-zangar sun jefi ‘yan sandan da gwangwanin giya, inda su kuma suka mayar da martani da hayaki mai sa hawaye da kuma ruwan zafi.

Matakin na ‘yan sandan ya raba jama’a zuwa kananan kungiyoyi wadanda suka kara yin arangama tare da kona shingaye da kwalayen shara kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Masu zanga-zangar sun bukaci a sauya matakan da gwamnati ta dauka na baya-bayan nan da ke bukatar jama'a su nuna takardar izinin shiga ta COVID-19 don shiga wurare daban-daban.

Yawancin kasashen Turai sun ga manyan zanga-zanga a cikin 'yan makonnin da suka gabata yayin da gwamnatoci suka matsa kaimi don sanya takunkumi mai tsauri don dakile barkewar sabuwar annobar COVID-19.

Fitowar sabon nau'in Omicron na coronavirus ya haifar da ƙarin damuwa, ya girgiza nahiyar.

Zanga-zangar da aka yi a ranar Lahadin da ta gabata ce ta sake maimaita muzaharar ranar 21 ga watan Nuwamba inda masu zanga-zangar suka yi artabu da 'yan sanda a Brussels, lamarin da ya yi sanadin kama mutane da jikkata wasu.

Zanga-zangar ta zo ne bayan sanarwar da aka fitar ranar Juma'a na sabbin matakai a zaman wani bangare na kokarin dakile kamuwa da cutar a Turai, gami da sanya abin rufe fuska na tilas ga yawancin yaran makarantun firamare da kuma tsawaita hutun makaranta.

_ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.