– Kafofin yada labaran Iraqi sun rawaito cewa an kai hari kan ayari biyu dauke da kayan aikin sojan Amurka a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Sabereen ya labarto cewa da yammacin yau alhamis an kai hari kan ayarin motocin sojin Amurka guda biyu a tsakiya da kuma kudancin Iraki.

An kai wa daya daga cikin ayarin motocin hari a lardin Babil (a tsakiya) dayan kuma a lardin Al-Diwaniyah (kudu).

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, kuma majiyoyin Irakin ba su fitar da wani rahoto na hasarar rayuka ko barna ba.

Rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da wasu majiyoyin na Iraki suka bayar da rahoton wani hari da aka kai kan ayarin motocin Amurka a kan iyakar Siriya da Iraki a 'yan kwanakin nan.

A cikin 'yan makonnin da suka gabata, jerin gwanon motocin sojojin Amurka masu yawan gaske sun shiga Iraki ta hanyar hadin gwiwa da kamfanonin Iraki ta mashigan kan iyaka daban-daban.

A halin da ake ciki, a 'yan watannin baya-bayan nan, an sha kai hare-hare kan ayarin motocin da ke dauke da kayan yaki na sojojin Amurka da ke jibge a sansanonin soji daban-daban a Irakin da bama-bamai a gefen hanya.

Kungiyoyin Iraqi da dama na daukar sojojin Amurka da ke kasar a matsayin 'yan mamaya tare da jaddada bukatar janyewar wadannan dakarun daga yankunansu nan take.


Ibn Tukur Almizan.
313 Resistance media