Ad Code

Responsive Advertisement

AN SABUNTA KIRAN NEMAN A SAKI SHEIKH ZAKZAKY [H] A GARIN GUSAU

 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
```FREEDOM_FOR_ZAKZAKY``` 📡
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

A Yau ne ranar  Alhamis 27 ga watan Disamba na shekarar 2018. Da misalin karfe 12:30 na safiyar yau; wasu ba'alin 'Yan uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky [H] na garin Gusau suka sake fitowa don gudanar da muzahara ta lumana tare da neman gwamnatin Najeriya ta gaggauta sakin malaminsu wato Sheikh Ibrahim Zakzaky [H] ba tare da wani sharadi ba!

Muzaharar ta taso ne daga babban masallacin Jumu'a (1) na garin Gusau  dake Kanwurin sarki   cikin tsari da kyakkyawan nizami, inda wasu 'Yan uwa suka daddaga hotuna masu bayyana irin harin ta'addanci da sojojin Najeriya bisa umarnin gwamnatin Buhari suka kaddamar akan Sheikh Zakzaky [H] da almajiransa, sannan suka kamashi suka mikawa jami'an DSS su kuma suke tsare da shi tun a watan Disamban Shekarar 2015 duk da kotu ta bada umarnin a sakeshi tun a shekarar 2016.
wasu daga cikin 'Yan uwan  kuma  suna tafiya ne suna rera wakoki da take daban-daban na kira ga gwamnati da ta gaggauta sakin Shehin Malamin don cigaba da tsareshi zalunci ne.

Daga nan aka doshi tsohuwar kasuwa zuwa Round about na Bello Bara'u. Sannan aka juya aka nufi titin Investment house, inda a nan ne aka gabatar da gangamin free Zakzaky  sannan daga bisani aka yi addu'a aka sallami kowa.

An dai fara wannan Muzahara lafiya kuma an kare lafiya!

✍ Sharief Munauwar Mukhtar
@gusaumediawatch


Post a Comment

0 Comments