________________________________
22 Rabi’ul Sani, 1440 - 30/12/2018
__________________________________
Dandalin Matasa na Harkar Musulunci A Najeriya Karkashin Jagoranci Sayyid Zakzaky (H) Yanki Jos (Zone) ta shirya taron karawa Juna sani (MU’UMTAMAR) karo na bakwai (7) a Garin Doma dake Jihar Nasarawa daga ranar Jumma’a 28 zuwa Lahadi 30 ga watan Disamba, 2018.
Taron wanda akayiwa taken: GINA SHAKSIYYAR MATASHI DAN Gwagwarmaya da kusanto da yayan ‘yan uwa ga Harkar Musulunci,
ya samu daman halarta Malamai daban daban kamar su Malam Tahir Doma, Malam Ahmad Tijani Azara, Alh. Dr. Sabiu Adam Keffi, Malam Aliyu Baba Salati daga garin Makurdi da kuma Wakili Matasa na Harkar Musulunci karkashin Jagoranci Sayyid Zakzaky (H) na kasa Alhaji Adamu daga Kano dukan su sunyi Jawabai aka maudu’ai daban daban musamman akan abinda ya shafi Abuja #STRUGGLES da kyawawan dabiu, salolin dare ga matasa harkar Musulunci, Wajimcin neman Ilimi da kuma aiki da shi, sani hadafi harkar da manufar Jagoran Sayyid (H) da dai sauran su.
Daga nan aka kai ziyara zuwa wata Cocin ECWA BISHARA dake nan gari Doma inda malami mujamiya yayi wa matasan kyakyawa tarba da farin ciki da godiya da kuma adduoin na musamma ga jagoran Sayyid (H) sanan ya ce yan uwa su cigaba da dakewa akan zalunci da akayima Jagoramu yace Allah da yayi duhu shine zaiyi haske tabbas Allah sai ya saka muku.
Daga nan aka koma wurin taron aka gabatar da tamsiliya sai kuma jawabi rufewa daga Malam Muhammad Nurudeen Ahmad wakili yan uwa na garin Lafiya wanda ya wakilce Sheikh Adamu Tsoho Ahmad Jos.
A cikin Jawabin sa Malam Muhammad Nurudeen ya bayana muhimmaci matasa a harkar nan da kuma aikin da ya hau kansu a wanna lokacin wanda kafirci duniya tayi hujumi akan Jagoran Harkar Allamah Sayyid Zakzaky (H). ya cigaba da cewa daga cikin hujumi kafirci duniya akan harkar nan shine raraba kan matasa da kuma shagaltar da su ga bari wajibi da ya hau kan su na gani fitowa Jagora Sayyid (H).
Da ya juya akan batun hakki jagora kuwa, Malam yace idan akwai wani yunkuri da ake yi na gani fitowa Jagora Sayyid (H), sai aka samu kowa a wannan yunkurin amma kai matashi baka je anyi da kai ba to Jagora yana binka bashi.
Ya kara karfafa yan uwa matasa wurin yawaita saurare Jawaban Jagora, yace yanda kake yawa ji wakokin harkar ko in baka ji ba a rana baka jin dadi to dole ya zama idan baka ji jawabi sayyid (H) ma ba kaji a hakan walau tafsirin sa ne ko sauran jawaban karatutukan sa masu albarka.
Wasu daga Hotuna da muka dauko maku a wurin taron:
22 Rabi’ul Sani, 1440 - 30/12/2018
Sale Haruna Nass

@LafiaMediaForum