Ad Code

Responsive Advertisement

Shekaru Shida (6) Da Kashe min Miji na, Har Yau Ban San Inda Mahaifina Yake Ba



- Daga Asma'u Muktar Sahabi

Na kasance daga cikin dimbin almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky da harin sojojin Nijeriya ya ritsa da su a Gyallesu, a yayin da suka zo da nufin kashe kowa da kowa matukar kowan nan zai musu shamaki ga isa kan Shaikh Zakzaky don su aiwatar da mugun nufinsu a kansa.

Tare da ni akwai Mijina, Shahid Muhammad Rabi’u, wanda a wannan lokacin watanninmu goma kacal da yin aure. Wannan rana ta Lahadi, 13 ga Disambar 2015, ita ta zama ranar karshe na ganin Masoyina, Emmar (kamar yadda nake kiransa) tare da cewa ban shirya ma rabuwarmu da shi a sannan ba, sai dai ma na yi burin ace tare aka kashe mu don mu je ga Allah muna wadanda aka zalunta aka raba mu da rayuwarmu bisa zalunci! Duk da hakan, rabani da aka yi da shi alhali muna tsananin son juna ya isa girman zaluncin da ko da ace mijina kawai aka kashe a Gyallesu bazan fasa addu’ar Allah ya gaggauta daukar min fansa akan duk mai hannu akan afka mana da aka yi ba!

A kullum kwakwalwata na bijiro min da lokacin da sojoji suka kashe daruruwan ‘yan uwan da ke gewayen gidan Abbah, har suka nufo shiga gidan a yayin da suka iso gaban gidan, a wannan lokacin Emmar dina, ya zo ya rikeni yana cewa; “Ummi zo mu tunkari mutanen nan, ba za su kyalemu ba.” Nace masa “Jikina ya yi sanyi ga kafata a daure da bandeji.” Yace shi kam zai tafi. Nace; “kar ka tafi.” Na rikeshi ina kuka, sai Sisters din da suke wajen suka rikeni suna cewa; “Ki kyaleshi ya tafi.” A nan ne Shahidi ya rike hannuna yace; “Ummi Allah ya kaddara saduwarmu.” 

A nan ne, wani soji guda daya da ya bullo kan layin gidan Abbah ya bude wuta a kan ‘yan uwan da ke kan layin, wannan tsinannen sojin ne ya harbe min Mijina da rayayyen harsashi a kirjinsa ta gefen dama.

Kamar ina ganin sadda Kanina Husaini da wasu ‘yan uwa suka daukoshi, suka yi baya da shi, suka ajiye shi a kofar gidan Malam Maina. Ko da na kariso inda suke,kamar ance in waiga sai naga mijina kwance cikin jini. “Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un! Sun kashe min shi!” Abin da bakina ke fada kenan a lokacin. Kamar yana ji na ina cewa “Ba haka mukai da kai ba Emmar dina. Tare muka ce za mu tafi.” Jini sai zuba yake daga jikinsa ina kallo, a sannan ba wani mai taimakona a kan tsayar da jininsa, saboda ‘yan uwa duk suna kwakkwance daga wadanda aka jikkata sai wadanda suka cika alkawarinsu. Masu ba da agajin gaggawa kuwa in ma da wadanda suka rage, babu kayan aiki a tattare da su a sannan. Sai ya zamana Bandeji kawai muka iya samu. 

 Har yau yana maimaituwa min sadda mijina ke min; “Ummi, kicewa kowa ya yafemin.” A yayin da yake cewa kanni na da suke kusa da shi; “Ku matsa Mala’iku sun zo mini” Jini yana ta zuba ta bakinsa da ta kirjinsa, da ka ga Emmar dina ka san harsashi ya riga ya masa illa. Nan ya fara Anbaton Allah, yana kalmar Shahada, da kiran sunayen A’imma (AS). Can sai ya koma Salati ga Manzon Allah (S). Bayan mun shigar dashi gidan Mal. Maina A tsakiyar hakan ya daga ido ya kalleni yace; “Ummi ki fita kawai.” Na kasa komai ina kallonsa har zuwa sanda naga Emmar dina ya yi nishi sau biyu a hankali tareda bude ido da baki, ya kalleni yana min murmushi, ya kulle bakinsa da ido a hankali wannan shine karshen numfashin Emmar dina. Inna lillahi wa inna ilaihi Raji’un! Nacewa ‘Sisters’ din da ke dakin; “Emmar dina ya tafi. Sun kashe min shi.” 

 Ta yaya zan mace da wannan bakin zalunci da a tsakar ranar Allah (T), ba mu san hawa ba bare sauka kawai wasu da suke mutane ne kamar mu su zo su dauki awanni sama da 48 suna bude mana wuta bisa zalunci? Kai kace muna kasar da ba abin da ake kira gwamnati, tare da cewa an san wadannan mutanen har yau ba wanda aka hukunta a cikinsu! Sai ma sauran ‘yan uwa na daruruwa da aka kama ake tsare da su har yau wasunsu ba mu san inda ake ma tsaren da su ba.

 Daga cikin ‘yan uwa daruruwan da sojojin Nijeriya suka kama suka tafi da su har yau babu labarinsu, baya ga aminaina mata (Sisiters) da muke tare da su, da dumbin burazu, akwai mahaifina Malam Muktar Sahabi, wanda babu wani dan uwa da ke da shaidar cewa sojojin sun harbe shi kamar yadda akwai irinsa da yawa da zarginmu ya karfafu akan cewa sun kama su ne da ransu, kuma suna nan boye a hannun sojoji ko sauran hukumomin kasar nan, sun hana mu sanin inda suke.

 Baba ina sane da kai. A kowane lokaci ina kewarka, ina kwadayin dawowarka daga wannan doguwar gaibar da azzalumai suka shigar da kai, tare da dukkan yan uwan da ke tsare a boye wanda na yi Imani cewa Allah ne kawai zai zama garkuwa a gare ku.

 Allah ne shaida akan cewa Jagoranmu, Shaikh Zakzaky da almajiransa wadanda suka kasance raunana, ba masu laifin komai bane, face hukumomi ne suka ga cewa su barazana ne ga mulkin zaluncinsu don haka suka mai da su abin farauta a kowane lokaci suna yunkurin ganin bayansu.

 Ban yafe ba! Na barwa Allah! Kuma hakika Allah shine mafificin masu sakayya. Cigaban rayuwata, insha Allahu tabbaci ne na cewa zan dauki fansar abin da akai wa Jagora na, rabani da aka yi da mijina, da mahaifina da kuma sauran ‘yan uwa na. “Kuma duk wanda ya aikata misalin kwayar zarra na sharri zai gani!”

Post a Comment

0 Comments