Ad Code

Responsive Advertisement

Dakarun ‘Isra’ila’ sun kai wa Falasdinawa hari, sun jikkata mutun 70 a Yammacin Gabar Kogin Jordan.


__ Dakarun mamaya na ‘Isra’ila’ sun raunata kusan Palasdinawa 70 a wani hari da suka kai birnin Nablus da ke yammacin gabar kogin Jordan, biyo bayan harin da ‘yan sahayoniyawan suka kai kan motocin Falasdinawa a yankin.

Kafofin yada labaran Falasdinu sun rawaito cewa an yi arangama tsakanin sojojin ‘Isra’ila’ da Falasdinawa a kauyen Burqa da ke arewa maso yammacin birnin Nablus a daren Lahadi.

A cewar hukumar bada agajin gaggawa ta Red Crescent ta Falasdinu, Falasdinawa 15 ne aka harba da harsashin roba yayin da wasu 52 suka fuskanci matsalar numfashi bayan shakar hayaki mai sa hawaye da sojojin yahudawan sahyoniya sukai amfani da su.

A ranar Lahadin da ta gabata, wasu Falasdinawa hudu sun jikkata a yayin wani hari da wasu Isra'ilawa suka kai kan motocin Falasdinawa a kusa da kauyen.

_ Mahadi Tukur Almizan.
313 Resistance media.

Post a Comment

0 Comments