Ad Code

Responsive Advertisement

Mu ba 'yan Gwagwarmayar Shi'anci ba ne; Mu 'yan Gwagwarmayar Addinin Musulunci ne.



Mu ba 'yan Gwagwarmayar Shi'anci ba ne; Mu 'yan Gwagwarmayar Addinin Musulunci ne.


Daga Nusaiba Ibraheem El- Zakzaky 

Ba sunana Musulma 'yar Shi'a ba, ni Musulma ce kawai, ba wani suna da za'a dora bayan sunan musulunci. Duk wani suna da zai rarraba al'ummar musulmi zuwa qungiyoyi ko wani abu sabanin musulmi, bai kamata mu (al'ummar musulmi) mu aminta da wannan sunan ba. Musuluncin da Annabi Muhammad (SAWW) ya zo da shi, daya ne tal.

Mu musulmi, bai kamata mu aminta da sunaye irin Dan Shi'a, Dan Sunna, Musulmin Nijeriya, Musulmin Amerika, Musulmi mai tsattsaura ko sassauqan ra'ayi ba da sauran su.

Akwai mamaki da ban takaici ganin yanda wasu 'yan uwa ke kiran abunda ya faru a Zariya da sunan kisan kiyashin 'yan Shi'a, kai kace, Gwamnatin ta kai mana harin ne saboda muna bin 'Mazhabar' Shi'a ne. Ai akwai mutane da suke bin 'Mazhabar' Shi'a amman ba'a kai masu harin ba.

Lokacin da aka fara wannan kiran, da yawan 'yan uwa 'yan Sunna ne, amman kuma duk da haka, Gwamnati a wancan lokacin ma bata kyalesu ba, ta masu duk irin abunda take mana a yanzu; kamu da dauri, kisa da sauran su.

Haka kuma, a wancan lokacin ma, Gwamnatin na ganin su a matsayin barazana ga tsarin su na danniya da zalunci, saboda mene? Saboda suna yunqurin ganin kawo qarshen danniyar da suke ma al'umma.
Da ace zamu yi shiru kan zaluncin da mahukunta ke yi, to da muma mun rayu lami lafiya ba wata matsala, da mun zauna lafiya; zaman lafiyar da babu 'yanci, sai dai qunci.

Babana bai taba kiran kansa da shugaban wata qungiya ba, kuma bai kira Harkar Musulunci da qungiya ba. Babbar manufar Harkar Musulunci shi ne, yunkurin kawar da wannan tsarin na zalunci da danniya da aka danqara mana a wanann kasar. Kiran kuma bai taqaita ga musulmi kadai ba, a'a har wadanda ba musulmi ba, dama duk ko daga ina mutum yake, to ana maraba da shi a wannan fafutukar.

Sannan koma dai wace irin 'Mazhaba' mutum yake bi, to daga karshe dai burin kowannemu shi ne yaga ya aikata addini irin addinin da Manzon Rahama (SAWW) ya zo da shi.

Ba da jimawa ba muka gama tarukkan makon hadin kai, taron da ake kiran musulmi masu kalar fahimtu daban-daban domin haduwa kan abunda ya hadamu da samun hadin kai, sabanin banbance-banbancen da ke Tsakaninmu na fahimta da rarraba. Kada mu bari abunda ya faru ya mantar damu abubuwan da muka dade muna koyo daga wannan taron.

Lokacin da aka kashe 'yan uwana uku (Ahmad, Hamid da Mahmud) a shekarun baya, an kashe su ne yayin da suke Muzaharar nuna goyon baya da tausayawa al'ummar Pasaldinu, wanda suke su Palasdinawa, mafiya yawansu mabiya Mazhabar Sunna ne. Ba an kashe su bane saboda wai suna bin 'Mazhabar' Shi'a ba, a'a sai dai don suna fada da zalunci.

Mahukuntan Nijeriya suna kallon wannan nuna goyon bayan ga Palasdinawa a matsayin barazana gare su, saboda suma din azzalumai ne, idan ba haka ba, a kan wane dalili za ku kashe masu zagayen lumana, wadanda basa dauke da makami, ku harbe su ku tsare su har sai da jininsu ya tsiyaye.

Abunda ya faru (a Zariya) ba kisan kiyashin yan Shi'a ba ne, kisan kiyashi ne kan musulmi kawai illa iyaka, kuma mutane ya kamata su yi tofin Allah tsine a kai, musulmi da wanda ba musulmi ba, musamman 'yan Nijeriya. 

Idan dai har Gwamnatin da tayi alqawarin kareka, Sojojinta zasu iya kashe ka kan abunda bai taka kara ya karya ba kamar amfani da sunan tare hanya, sannan kuma har su iya fitar da bidiyo wanda a wurinsu, zai zama hujja kan kashe daruruwa ko dubban mutane, to mene kuma ba za su iya kashe ka a kansa ba? Idan har ka yi shiru kan abunda ke faruwa na zalunci, watarana kaima zai iya faruwa a kan ka, wa kake tunanin zai yi magana akai?

Fassara: Maigari
________________________
JAGORAN GASKIYA RESISTANCE MEDIA

Post a Comment

0 Comments