Idan ka karanta jawabin Jagora (H) na Shelar Funtua wanda ya gudana shekaru 40 da suka gabata, za ka ga yadda baro-baro Malam (H) ya bayyana da'awar nan.

Jagora ya cigaba da kira ne a kan wannan turbar na tawaye ga tsarin da ya sabawa na Allah da yunkurin tabbatar da addinin Allah a doron kasa. A karshen shekarun 1980s, bayan yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky sun dan fara auki, magoya baya sun fara yawa, wasu sun fara zuwa da wasu maganganu na cewa, me zai sa ba za a shiga tsarin siyasar kasar nan ba, ala bashi sai a kawo gyara a cikin siyasar ta hanyar canza ta daga tsarin Bature na kafirci zuwa na Alkur'ani da dokokin Allah?

Shigen yadda wasu a yanzu suke kokarin cewa zaluncin da mahukuntan kasar nan suke mana ya yi yawa, me zai sa ba za mu shiga cikin tsarin bane, ko muma mu wakilta wakilanmu a ciki, mu yi zabe, mu zama 'Yan Dimukuradiyya, sai ya zama muna da Gwamnoninmu da yan Majalisu da masu rike da manyan mukamai, wai a zatonsu ta haka yan uwa masu gwagwarmayar addini za su samu sauki daga fada da su da tsarin Kafirci ke yi a kan yunkurinsu na rusa tsarin na Baturen Ingila da tabbatar da tsarin Allah (T).

Ban sani ba, ko suna nufin akwai wata hanya 'shortcut' ce da Harka Islamiyya za ta bi sai ya zama ta samu sauki daga azaba, takura, kamu kisa da daurin azzalumai, kuma ta haka har addini ya daukaka ya dawo daram ya cigaba da iko da doron kasa?

Ga wani yanki na jawabin Jagora, Shaikh Ibraheem Zakzaky dangane da masu ra'ayin cewa za a shiga Siyasar Nijeriya sai a kawo gyara, a kawo adalci, a shimfida Musulunci, a dena barna da zalunci a ciki. Ya yi jawabin ne a shekarar 1989, kimanin shekaru 29 da suka gabata:

BANGAREN JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY GA MASU TUNANIN A SHIGA TSARIN KAFIRCI A KAWO GYARA:

"Da'awar cewa ka hadu da ma'abota tafarkin bata, ka bi tafarkinsu kafin ka kawo gyara, kira ne irin na Shaidan. Domin yana iya yiwuwa kana yin bata da sunan za ka kai ga shiriya sai mutuwa ta riske ka, ka gamu da Allah baka da hujja.

"Ba mu bukatar mu bi ta hanyar bata, domin mu kawo shiriya. Ba wani Manzo da Allah (T) ya aiko domin ya kira al'ummar sa ta dena wani barna ko wani nau'i na fasadi da ya zama mishi wajibinsa ya shiga ai barnar ko ai fasadin tare da shi domin ya kawo gyara.

"Yayin da Annabi Nuhu (AS) ya samu al'ummar da aka turo shi gare ta a kan fandara daga tafarkin Allah, ba sai da ya fandare tare da ita sannan ya kira ta izuwa ga tafarkin Allah ba. Yayin da Allah (T) ya aiko Annabi Ibraheem (AS) don ya rusa gumaka, ba sai da ya bautawa gumaka ya zama limamin bautar gunki ne, sannan ya rusa ba. Kai tsaye ne ya je ya rugurguza! Suka kuma rugurguzu. Ba shi yiwuwa Allah (T) ya aiko Annabi Ibraheem (AS) don ya rusa gumaka Sai Kuma ya je ya bauta musu, sannan yace ma mutane to Kun ga dai muna yin bautan nan tare ne ko? To yanzu a ba dena. Ba nine limaminku a wajen bautan ba? To bashi da kyau. Tunda yake ya salladu a kan su Sai kawai su bi zancen sa. Ba zai yiwu ba.

"Ba shi yiwuwa ga Annabi Ludu (AS) wanda Allah ya aiko ya gargadi mutane da aikata wannan mummunan aikin ya zamto kuma shima ya shiga an yi wannan mummunan aikin tare da shi (Wal'iyazu Billahi) wai domin ya nunawa mutane wai wannan aikin bai kamata ba, mummuna ne. Komai tunaninka, ba za ka sauwala cewa Annabi Lud zai aikata wannan aikin ba.

"Ba shi yiwuwa ga Annabi Shu'aib (AS) wanda Allah ya aiko ya kira mutane su dena tankware mudu, ya zama shi ma ya zama ma'auni, ya dan mokade mudun nasa, shima sai ya zama Sarkin masu awo, ya kuma zama Jagoran matankwara mudu, sannan yace duk ba muna tankware mudu ba? Suce eh. Yace to daga yau mu bari.

"Ina fadin wannan ne don in nuna wawanci da sakarci da karancin tunanin wanda yake ganin cewa sai mun shiga tsarin da ya sabawa na Allah, mun jagorance shi, kafin mu dawo da Musulunci. Ba mu bukatar mu shiga barna mu zama mabarnata wai domin mu yi gyara. Wannan barna ko da shekara dubu nawa aka yi ana dasa ta a rana daya muna iya cewa ba mu yarda da ita ba, kuma shikenan karshenta ya zo!

"Yanzun Musulmin da ke kasar nan, kamar miliyan 70 ko fiye, wanda aka dankara musu kayan Kafirci, niki-niki suna da daukansa, in yau suka ce bamu so. Wane ne ya isa ya dankara musu? Dalilin da yasa aka dankara musu wannan kayan na Kafirci suke dakonsa niki-niki sun yarda su dauka ne, in suka yarfar ya yarfu. Dalilin da yasa kaga ana nan a fandara, saboda al'ummar ta yarda ta dauki fandarar ne.

"Kuma ma in ka lura da mu da kyau za ka ga a bisa gaskiya ayyuka da zantukanmu sun nuna mun amshi barnar nan. Saboda mene? Ga wani abu an ce shi ba addinin Musulunci bane, ba ruwansa da addini, amma kuma aka ce mu yi wai a matsayin dabara ce ta dawo da addini. Ga doka ba ta Allah bace, ba ta Musulunci bace, an ma bayyana cewa Dokar nan fa ba ta Allah bace, kuma ba ruwanta da addini, amma muka dage muka ce a bi. Ya zama yau in mutum ya mike yana da'awa izuwa Musulunci, Sai ya rika kakkawo wasu ra'ayoyi na cewa akwai mu da bukatar mu rika wannan tsarin ne, saboda 'ya'yan Anna ne sukai mana yawa, su suke rike da manyan mukamai. *Mu kame mukamai a soja, mu kame na yan sanda, mu kame na manya-manyan ma' aikatan Gwamnati, mu sa Shugaba ya zama namu, Gwamnoni su zama namu, manyan ofisoshi da komai da komai su zama namu, sai mu maishe da abin addini. Amma kafin mu mayar din mun san ba addini bane mu da kanmu, amma mu yi hakan a matsayin dabara.*

"To, in ka ce haka nan ne, Sai nace a bisa gaskiya kai mai fadin wannan ma baka da tunani!...

"... Ballantana ma, yanzu wane ne shugaban kasa? Musulmi ko? Wane ne Baban kwamandan soja? Musulmi ko? Wane ne mataimakin babban kwamandan soja? Musulmi ko? Wane ne mininstan tsaro? Kai har Pertol da ake hakowa a Potakwal wane ne mininstan Fetur? Musulmi ko? Masu kula da sha'anin tsaro? Musulmi! Babban Inspector na yan sanda, Musulmi. Alkalin Alkalai, Musulmi ko? Ahaf! Muna jira kuma sai mun samu Massenger Musulmi ne sannan za mu yi Musulunci?

"Haba Mutane, Sai mutum ya zauna da son rai. Yana ji yana gani ga addini, amma don ba zai yi ba yai ta surutu da kwana-kwana, yana cewa yanzu ba lokacin sa bane a yi kaza ne? In mutum ya lura da kyau masu kawo Hujjojin nan ya yi kama da ba addinin suke so ba. Suna so su kauce ma addinin ne kawai, suna kawo wasu uzurori da za a kauce ma addinin amma da sunan cewa ta wannan hanyar ne za a yi addinin."

— Saifullahi M Kabir