""Hakika naga dukkan abunda kace a Bidiyon da aka fitar na minti takwas (8). Lallai Ni banyi mamakin ganin kalamanka na rashin kunya akan Jagoran Harkar Musulunci Sheikh Zakzaky ba, domin ita tarbiyyah ana samunta ne tun daga gida kuma lallai bana tunanin ka samu wannan tarbiyyar domin kuwa mai Tarbiyyah baya Yaudara ballanta cin Amana, baza ka ga wanda ya samu Tarbiyyah daga gida ya zagi na gaba dashi musamman Wanda ya masa halarci, wannan kuma ba komai bane a wajen Nasiru, domin kuwa abunda kayi ma Uban gidanka Obasanjo ya nuna mana haka, haka kuma ka zagi Sardauna, to kaga Zagin Manya ai ba komai bane a gareka don ina da tabbacin duk wanda kaga yana zagin kowa to kada kayi mamakin ya zagi Iyayensa ma da suka Haifeshi.

Dukkan wasu Surkulle da sako burutsun da kake yi kana yi ne domin mutanen Kaduna su yarda dakai a matsayin kai ba Dan Ta'addah bane, abunda kuka yi a Zaria da Kaduna Sunansa Ta'addanci kuma duk wanda ya bada gudunmawa wajen gudanar da wannan aikin sunansa Dan Ta'addah saboda haka da Buhari da kai Nasiru da Buratai da dukkan wadanda suka taimaka muku wajen wannan aikin sunsanku yan Ta'addah, Al'ummar Jihar Kaduna mun Dade da gane hakan. To wai kuma a hakan kake son ka sake zama Gwamnan Jihar duk da abubuwan da kayi na Ta'addanci da wargaza Jihar?

Cikin magananka kayi magana akan Shi'a to mu ka sani Musuluncin da Manzon Allah yayi na Gwagwarmaya da Azzaluman Kafirai muma shi zamu yi a Kasarmu ta Nijeriya, Nijeriya Kasarmu ce kuma baka isa kace dole sai mun bika ba, ko kuma sai mun bi Uban gidanka Buhari ba, mutane nawa ne a Kasar nan basu da katin zabe kuma basu yin zabe a Nijeriya kuma ba yan Harkar Musulunci bane?
Da kace bamu yarda da Kasar ba, shin bamu aikin Gwamnati? Sunanmu yan Gwagwarmayar Musulunci (Islamic movement in Nigeria) kuma kai baka isa ka canza mana suna ba.

Da kace Jagoranmu Sheikh Zakzaky ya cire rawanin yazo ya kasance tare daku, kaima ka kasan cewar da Sheikh Zakzaky Mulki yake so da sai dai kai ka kasance mai wanke masa Mota, domin kuwa babu Sa'ansa a cikinku bangaren Ilimin Addnin dana Bokon, kaje Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria (ABU Zaria) ka sake tambaya. Shi kuma kirista da kake magana a kansa me kake so ayi masa, a kashe shi ne? Wannan ne ya kara tabbatar mana da Kaine kake hada dukkan fadace-fadacen da akeyi a Kaduna, da kayi Karatun Addini da sai in tambaye ka shin Manzon Allah bai zauna da Kiristoci ba?

A cikin Wasiyyar Manzon Allah yace, Ku girmama dukkan Mutane harda Kiristoci in mutum ba Dan Uwanka bane na Addini to Dan Uwanka ne Dan Adamtaka kai Mutum ne kuma shima Mutum ne kuma dukkan Ku kuna da Daraja a wajen Allah saboda haka Ku girmama Junanku. Nasiru naji dadin Kalmar da kayi na cewar Mutum nada damar yayi Addininsa amma ina ganin wannan ga sauran yan Kasa ne kawai banda yan Harkar Musulunci ko? Domin kuwa naga kullum in suka fito koda a Muhhalansu ne da suka siya da Kudinsu afka musu kake sawa ayi, In kayi magana akan tare hanya shin lokacin da kake Neman wannan Kujerar baka tare hanya ba? Ina da tabbacin da kana da hankali da tunani kuma baka yi shaye-shayen daka saba ba kuma da kana tunanin baya baza kayi wannan maganan ba.

Da kana tuna baya Nasiru ina da tabbacin da baza kace an hana wani shiga Gyallesu ba, lokacin da kaje ka durkusa a gaban Sheikh Zakzaky kana masa Ta'aziyyah ta ina ka shiga? Lallai na kara Gaskata zancen Barista Alex da yake cewar ka kiyayi mutumin da kaga zai gaishe ka yana durkusar da kai amma Idonsa a sama, lallai ka kara tabbatar da kansa munafuki Nasiru, to kaje Gyallesu yanzu haka ka tambayesu yanda suke fama da barayi da yan Daba ba kamar a baya ba. Da kayi magana akan karya doka tun daga nan nasan kawai kana Nijeriya ne amma baka San dokokin Nijeriya ba, shin zaka iya gaya mana Abu guda daya da muka taba yi wanda ya saba ma dokar Kasar?

Ta'addancin da Sojojin Nijeriya karkashin Jagorancin Lt. Kanal Tukur Buratai suka yi na Kashe sama da mutum dubu ciki kuwa harda yara da Mata masu ciki da sa hanunka akayi, Amerika da Isra'ila da Saudiyyah ne suka bayar da kwangilar Kashe Sheikh Zakzaky da Almajiransa kuma Buhari da Buratai da kai Nasiru kune kuka karbo wannan kwangilar saboda haka baka da hujjar da zaka kare kanka akan wannan aikin. Kace kunyi Shekaru biyu Kuna bincike akan abubuwan da Sheikh Zakzaky yayi a cikin wannan bidiyo din, amma shin kwamitin daka kafa na JCI me ta tabbatar maka?

Maganan Kotu kuma yana da kyau ka tuna cewar babban Kotun Kasa ta baku Umurnin Ku saki Sheikh Zakzaky da Mai dakinsa kuma Ku biya shi diyyar Miliyan 50, sannan Ku Gina masa gida a duk inda yake so, amma kun bijire ma wannan Umurnin ba tare da kun daukaka kara ba sai da lokaci ya kure kuka sake cewar kun kai Sheikh Zakzaky kara  kuna tuhumarsa da wasu abubuwan da babu kan gado ma kuma a Jihar Kaduna, hakan ya kara nuna mana kuna da wata manufa akan Sheikh Zakzaky shiyasa kuka ki bin Umurnin Kotu, kwangilar da aka baku na Kashe shi kuke so Ku cika ma iyayen Gidanku alkawarin da kuka dauka musu.

Maganan Kisan kai kuma wanda ka Kashe masa 'Ya'ya da Almajirai ne kake tuhumarsa da aikata kisan kai? Sannan kama yara da kace Sheikh Zakzaky nayi, shin ka dauka abunda kake yi kowa nayi ne? Kaine mai Garkuwa da Mutane a dajin birnin Gwari da cikin garin Kaduna da sauran yankunan garin akwai Hujjoji da daman gaske akan hakan, Aisha Taraba tayi wannan maganan ka Kasa fitowa ka kare kan ka da hujja. A gidan Sheikh Zakzaky babu wanda aka taba masa hakan, duk wanda kaga yana tare da Sheikh Zakzaky to shine ya kawo kansa domin yaga Sheikh Zakzaky ne kadai Mafitar Kasar nan ba Ku ba.

Kace Gwamnatin Nijeriya bata da Matsala da Shi'a har ka kawo wani mai suna Hamza Lawal to ai dama ba Shi'a bane baku so, Musulunci ne Baku son ayita yanda Manzon Allah yazo da ita, kuma kunga Sheikh Zakzaky yana kirane akan azo ayi ta shiyasa kuke afka masa, shin zaka iya gaya mana a dukkan Jawaban Sheikh Zakzaky inda yace azo ayi Shi'a? Babu wannan maganan a dukkan Jawaban Sheikh Zakzaky. Sai dai yace "Kuzo muyi Gwagwarmayar Musulunci." Kuma dama ai bai boye muku komai ba Nijeriya Kasarmu ce kuma zamu kwace wannan na Sheikh Zakzaky ya fada muku ai, Hamza Lawal kuma wannan ai kayan aikinku ne, idan an gama shan abun sha me za'ayi da kwalban? To haka Hamza Lawal ma ranar da kuka kammala aiki dashi Ku zaku Kashe shi kamar yanda kuma ranar da Amerika da Isra'ila zasu Kashe Ku.

Da wani doka Nasiru kuka yi amfani wajen Haramta Harkar Musulunci ko tsare Almajiran Sheikh Zakzaky shekara 7 idan suka fito muzahara? A cikin dokokin tsarin mulkin Nijeriya babu Inda akace an hana Harkar Musulunci domin in haka ne dole a hana Sallah, tunda shima duka yana cikin Harkokin Musulunci ne, da kace Mulki Muke so Nasiru yau da Mulkine a gabanmu kai kan ka da baza kazo wannan Kujerar ba domin muna da wadanda suka fika a komai amma fa banda Ta'addanci domin Ni dai ban taba ganin Dan Karamin Mutum sai son zubar da Jini ba kamar ka, kai kace Yahudawane suka tsugunna suka haife shi.

Ni dai banyi mamakin dukkan abunda ka fada ba, domin Sanin Asaline yasa Kare Sidar Alli, zamu ci gaba da gudanar da dukkan abubuwan da muke yi kamar yanda dokar Kasa ta tanadar domin kuwa kai baka isa ka hanamu komai ba, Kamu ko kisa ko dauri bazai taba hanamu Addini ba, yana da kyau ka dinga tunawa da wannan a duk inda kake.

Ashe kasan baza ka zarce ba shiyasa kace zaka koma cikin Iyalenka, shin kana tunanin zaka kammala dukkan wannan Ta'addancin kuma ka koma cikin Iyalenka ka zauna lafiya bayan ka Kashe ma wasu Iyaye da 'Ya'ya ko? Yana da kyau ka dinga tunanin wannan maganan akan bazai yiwu ba Nasiru.

A karshe ina tunatar da kai ka sani, Baza ka taba Kashe mutane kai kuma ka zauna lafiya ba.

Daga Yahaya Muhammad Soje

Yahaya Muhammad Soje, Dan Jarida kuma Marubuci. Zaka iya samunsa ta (sayeedyahaya01@gmail.com.)